’Yan jarida sun kaurace wa gwamantin Kano
Ƙungiyar ta koka kan yadda ta ce gwamnatin jihar na cin zarafin ‘yan jarida a jihar.
Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai a ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jarida reshen jihar Kano, ta ƙauracewa ɗaukar ayyukan gwamnatin jihar kan zargin cin zarafin ‘ya’yanta.
Wannan na zuwa ne bayan wani taro da shugaban ƙungiyar a jihar, Aminu Ahmed Garko, ya kira a ranar Litinin.
- Mafi Karancin Albashi: Akwai yiwuwar komawa Yajin aiki
- Ana zargin Hajiyar Jihar Najeriya ta kashe kanta a Saudiyya
Taron wanda da manema labarai suka halarta, martani ne kan cin zarafi da ƙungiyar ta ce gwamnatin jihar ke yi wa ’ya’yanta, yayin da suke gudanar da ayyukansu.
“Duk da ƙoƙarin da muke yi na yi ganawa da gwamnati da jami’anta don magance wannan matsala, amma babu wani ci gaba da aka samu.
“Mambobin ƙungiyar na ci gaba da fuskantar tsangwama, tsoratarwa, har ma da cin zarafi yayin gudanar da ayyukansu.
“Abun damuwa ne yadda gwamnatin ta fifita wasu a kan ƙwararrun ‘yan jarida kan ayyukansu.
“Saboda haka, muna baƙin cikin sanar da cewa ba za mu ƙara ɗaukar rahoto ko wasu al’amuran da suka shafi gwamnati ba, har sai mun ga canji game da ‘yancin ‘yan jarida.“
Ƙungiyar ta buƙaci ɗaukacin ’yan jarida a jihar da su shiga zanga-zangar adawa da cin zarafin da ake yi musu a jihar.
“Mun yi imanin cewa bai wa ’yan jarida damar gudanar da ayyukansu na da muhimmanci ga dimokuraɗiyya, kuma ba za mu zuba ido ana cin zarafin ’yan ƙungiyarmu ba,” in ji sanarwar.