’Yan jarida sun kaurace wa buda-baki da Gwamnan Jigawa

Wakilan Kafafen Watsa Labarai da ke aiki a Jihar Jigawa sun kaurace wa shan ruwan da Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya shirya musu a ranar Talatar makon jiya.Hakan ya biyo bayan rashin fahimtar juna ne da ke tsakanin gwamnatin da kungiyar wakilan kafafen watsa labarai da ke aiki a jihar.Matakin da ’ya’yan kungiyar suka […]

’Yan jarida sun kaurace wa buda-baki da Gwamnan Jigawa

Alhaji Sule Lamixo, Gwamnan Jihar JigawaWakilan Kafafen Watsa Labarai da ke aiki a Jihar Jigawa sun kaurace wa shan ruwan da Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya shirya musu a ranar Talatar makon jiya.
Hakan ya biyo bayan rashin fahimtar juna ne da ke tsakanin gwamnatin da kungiyar wakilan kafafen watsa labarai da ke aiki a jihar.
Matakin da ’ya’yan kungiyar suka dauka na kaurace wa buda-baki da Gwamnan bai yi wa gwamnatin dadi ba, inda kakakin Gwamnan Malam Umar Kiyari Jitau Madamuwa ya yi ta bin shugabanin kungiyar yana rarrashinsu don su halarci shan ruwan.
Amma sai ’ya’yan kungiyar suka ki inda suka amsa gayyatar shugaban Jami’ar Tarayya da ke Jihar Jigawa Farfesa Jibiril Aminu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar wakilan kafafen watsa labarai da ke jihar Malam Ahmed Abubakar ya ce matsalar ’yan jarida da gwamnatin jihar ba wani boyayye abu ba ne, mukarraban gwamnati ne ba su bukatar su gan su a kusa da Gwamnan.
Ya ce wata matsala da ta hana su zuwa gayyatar da Gwamnan ya yi musu ita ce, wajen shan ruwan ana cakuda su da maroka da ’yan jagaliya ko ’yan dabar siyasa a lokacin shan ruwa da Gwamnan.
Ya kara da cewar saboda haka ne suka ki halartar wurin shan ruwan na gidan gwamnatin.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Gwamnan Malam Umar Kiyari cewa ya yi a saninsa babu wani abu da ya faru tsakanin gwamnatin jihar da wakilan kafafen watsa labaran.
Ya tabbatar da cewa wakilan kafafen watsa labaran sun ki amsa gayyatar da gwamnatin jihar ta yi musu na zuwa shan ruwan, kuma bai san dalilin kin zuwansu shan ruwan ba.