’Yan jarida za su fara yin rakiya ga sojin Najeriya

Ministan ya bayyana cewa, kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina ra’ayoyin jama’a game da ayyukan tsaro da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin ƙasa

’Yan jarida za su fara yin rakiya ga sojin Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazari kan wani sabon tsari da zai bai wa ’yan jarida damar yin rakiya ga dakarun sojin Najeriya a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki.

Rahotan na cewa, hakan zai ƙara bayar da rahotanni kan tsaro da tabbatar da abin da ake faruwa kan sha’anin tsaro.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Ministan Tsaro, Christopher Musa ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan tsaro da Ƙungiyar ’yan Jarida ta Najeriya, ta shirya a Abuja.

A cewarsa matakin zai ƙara fahimtar da jama’a ayyukan da sojin ƙasar ke yi, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman da ya wakilce shi a wajen taron Rear Admiral Olusanya Bankole, ya sanar.

Ministan ya ƙara da cewa, hakan zai inganta yadda ’yan jarida ke bayar da rahotanni kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da matsalolin tsaron cikin gida.

Ministan ya bayyana cewa, kafafen yaɗa labarai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina ra’ayoyin jama’a game da ayyukan tsaro da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin ƙasa, inda ya ƙara da cewa tafiyar da al’amuran tsaro a halin yanzu ya wuce batun fagen fama na gargajiya.

Ya bayyana cewa rikice-rikice na zamani suna matuƙar tasiri da bayanan da ake yaɗawa da kuma yadda ake bayyana labarai, wanda hakan ya sa kafafen yaɗa labarai zama muhimman abokan tarayya a cikin tsarin tsaron ƙasar.

A cewar ministan, bai kamata a auna nasarar ayyukan tsaro kawai ta hanyar samun galaba na soji a fagen fama ba, har ma da irin ƙwarin gwiwa da amincin da ’yan ƙasa suke da shi ga hukumomin tsaro.

Ministan ya ce: “Fiye da kowane lokaci, kafafen yaɗa labarai ba wai kawai masu taimakawa ba ne; su ne masu tabbatar da daidaito da ɗorewar gwamnati.