’Yan jarida za su shiga yajin aiki saboda tsadar man fetur

NUJ ta ce ba gudu ba ja da baya matukar NNPCL bai janye karin farashin man fetur da ya yi ba.

’Yan jarida za su shiga yajin aiki saboda tsadar man fetur

Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) ta ce za ta tsunduma yajin aiki daga ranar Laraba mai zuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Wannan dai na zuwa ne yayin da a Larabar makon goben Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC za ta tsunduma nata yajin aikin da ta ayyana saboda makamancin wannan dalili.

NUJ ta bayyana shirinta a cikin wata takarda da ta fitar, bayan ganawar da Kwamitin Gudanarwarta ya yi da safiyar ranar Asabar domin tattauna batun cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta yi da kuma matakin da Kungiyar Kwadago ta NLC ta dauka na shiga yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

Sanarwar da NUJ ta fitar

Kungiyar ta NUJ ta ce a halin da ake ciki tashin farashin man fetur da na sauran kayayyaki sun jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali.

Haka kuma, kungiyar ta umarci mambobinta da ke fadin jihohin kasar da su fara yajin aiki tare da fita zanga-zanga daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni matukar kamfanin mai na kasar NNPCL bai janye karin farashin man fetur da ya yi ba.

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani