’Yan jaridar Aljazeera: Masar ta ajiye ranar fara sauraron daukaka kara
Wata kotu a kasar Masar ta bayyana 1 ga Janairun badi a matsayin ranar fara sauraron daukaka karar da ’yan jaridar gidan talabijin na Aljazeera da aka daure a kasar. Wani daga cikin iyalan daya daga cikin ’yan jaridar Mohamed Fahmy da aka daure ne ya bayyana haka ga gidan rediyon BBC Landan, inda ya […]
Wata kotu a kasar Masar ta bayyana 1 ga Janairun badi a matsayin ranar fara sauraron daukaka karar da ’yan jaridar gidan talabijin na Aljazeera da aka daure a kasar.
Wani daga cikin iyalan daya daga cikin ’yan jaridar Mohamed Fahmy da aka daure ne ya bayyana haka ga gidan rediyon BBC Landan, inda ya ce babbar Kotun Masar za ta saurari karar.
An daure ’yan jaridar uku da ke aiki da gidan talabijin din mai mazauni a katar shekara bakwai a ranar 23 ga Yunin bana, bisa zarginsu da yada labaran karya tare da goyon bayan kungiyar Ikhwanul Muslimina.
Kotun tana iya tabbatar da hukuncin kotun baya, ko kuma ta sake shari’ar, kuma ana sa ran ta yanke hukunci a zama daya ko biyu, na sauraron shari’ar.
Wani lauya da ke da masaniya kan shari’ar ya shaida wa BBC cewa idan kotun ta yi watsi da hukuncin za a maido shari’ar zuwa kotun manyan laifuffuka don sake yin shari’ar.
Kuma idan ta tabbatar da hukuncin, to abin da ya saura shi ne a jira ko Shugaba Abdel Fattah al-Sisi zai yi musu afuwa.
dan kasar Masar babban jami’in gidan talabijin din a kasar Kanada, Mista Fahmy da wakilinsa na Austireliya Peter Greste da kuma mai tsara shiri na Masar, Baher Mohamed an kama su ne a watan Disamban bara.
An kara wa Fahmy daurin shekara uku kan tuhumar mallakar “harsasai ba tare da lasisi ba.”
Kuma yayin shari’ar an daure wasu ’yan jarida 11, ciki har da na kasashen waje uku a bayan idonsu na tsawon shekara goma-goma.
daure ’yan jaridar uku ya haifar da koke-koke a sassan duniya tare da jawo nuna damuwa kan yadda ake takura wa manema labarai a kasar Masar.
’Yan jarida a sassan duniya sun yi zanga-zangar tare da rufe bakunansu don nuna adawa kan daure su.