’Yan jaridar da aka sace a Kaduna sun kuɓuta bayan mako guda
Sun kuɓuta ne bayan shafe mako guda da sace su.
Wakilin jaridar ‘The Nation’ Alhaji AbdulGafar Alabelewe da iyalansa da kuma wakilin ‘Blueprint’ AbdulRaheem Aodu da aka sace a ranar 7 ga watan Yuli, sun kuɓuta bayan shafe mako guda da sace su.
’Yan jaridar da iyalansu an sace su a gidajensu da ke yankin Danhonu a rukunin gidaje na Millennium City da ke ƙaramar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
- Meta ya ɗage takunkumin da ya sanya wa Trump a Facebook da Instagram
- Abba ya bai wa mata 5,200 jarin miliyan 260 a Kano
Daga baya maharan sun sako matar AbdulRaheem.
Da yake tabbatar da sakin nasu, ɗan uwan AbdulGafar, Barista Mas’ud Mobolaji Alabelewe, ya ce an sake su kuma sun karɓar kulawa a Abuja.
Ya ce iyalansu suna jira dawowarsu idan sun kammala karɓar kulawa.
Ya ce: “Mun gode wa Ubangiji an saki ’yan uwanmu. Mun kwashe mako guda cikin damuwa amma mun gode wa Allah yanzu sun kuɓuta.
“Muna yi kowa godiya kan yadda suka taimake mu da addu’o’i a wannan lokaci.”
Kazalika, shugabar ƙungiyar ’yan jarida ta Jihar Kaduna, Asma’u Yawo Halilu cikin wata sanarwa ta bayyana jin daɗinta na sakin ’yan jaridar.
Ta ce: “Cikin farin ciki muna yi wa Allah godiya, abokan aikinmu AbdulGafar Alabelewe da AbdulRaheem Aodu da iyalinsu sun kuɓuta.
“Ƙungiyar tana miƙa godiyarta ga Kwamishinan ’yan sandan Kaduna, ofishin NSA, DSS, Sufeto Janar na ’yan sanda, gwamnatin Jihar Kaduna, shugaban NUJ da dukkanin ’yan Najeriya da suka taya mu da addu’a.
“Ba da daɗewa ba za mu sanar da lokacin da za su kasance tare da mu a Kaduna, mu yi farin ciki da sakinsu.”