’Yan jarida na fuskantar barazana daga coronavirus

A yayin da ake ci gaba da samun wadanda suka harbu da cutar coronavirus a Najeriya, kwararru sun bayyana damuwa a kan yaduwa zuwa wasu sassan kasar inda ake samun cunkoson jama’a. A lokaci guda kuma, ‘yan jarida wadanda su ke da nauyin neman labarai a kan batun suna fuskantar fargaba da barazanar kamuwa da […]

’Yan jarida na fuskantar barazana daga coronavirus

‘Yan jaridu

A yayin da ake ci gaba da samun wadanda suka harbu da cutar coronavirus a Najeriya, kwararru sun bayyana damuwa a kan yaduwa zuwa wasu sassan kasar inda ake samun cunkoson jama’a.

A lokaci guda kuma, ‘yan jarida wadanda su ke da nauyin neman labarai a kan batun suna fuskantar fargaba da barazanar kamuwa da cutar.

Yanayin aikinsu dai ya danganci ganawa da mutane daban-daban ba tare da sanin ko suna dauke da cutar ba.

Wasu ‘yan jarida da suka zanta da Aminiya sun bayyana yadda suke kaffa-kaffa da wuraren da suke zuwa da kuma mutanen da suke hulda da su idan sun fita daukar labarai inda suka bayyana cewa, sun karfafa amfani da matakai da kayayyakin kariya.

Wani dan jarida a Maiduguri da ke aiki da gidan talabijan na TVC, Jesse Tafida, ya ce rahotanninsa sun fi mayar da hankali a kan halin da ake ciki na cutar coronavirus da kuma dokar zaman gida da aka kafa saboda bai wa masu kallo cikakken bayani, amma yanayin ya kawo matukar sauyi a kan yadda yake gudanar da aikinsa.

“Akwai ‘yar fargaba duk da cewa muna amfani da matakan kariya kamar: kyallen rufe fuska da safar hannu da man wanke hannu da kuma ba da tazara a yayin da muke ganawa da mutane.

“Ma’aikatarmu ta ba mu duk abin da muke bukata a wannan bangaren. Babbar matsalarmu ita ce samun wadanda za mu gana da su a lokacin da dokar zaman gidan take aiki, amma dai muna kokari sosai”, in ji shi.

Wani ma’aikacin jaridar Daily Trust da ke daukar rahotanni a birnin Abuja, Adamu Umar, ya ce duk da cewa yanayin da ake ciki bai hana shi gudanar da aikinsa ba, yana amfani da matakan kariya sosai saboda kauce wa harbuwa da cutar.

Shi ma Ado Abubakar, wanda dan jarida ne da ke birnin Jos a jihar Filato, ya ce ma’aikatarsa da kuma kungiyar ‘yan jarida reshen jihar suna ba shi cikakken goyon baya a kan matakan kariya saboda ya kare kansa daga kamuwa da cutar yayin gudanar da aikinsa.

A nashi bangaren, Saminu Sani, wanda yake aiki da gidan talabijin da rediyo na Liberty, ya bayyana fargaba game da cutar ta yadda take da saurin yaduwa tsakanin jama’a duba ga yanayin aikinsa.

Ya ce, “Kamar sauran mutane, mu ma muna fargabar abin da ka iya faruwa. Ta kawo matukar sauyi a kan yadda muke hulda da wadanda suke ba mu labari har da ma iyalanmu.

“Yanayin aikinmu ya sa muna fuskantar barazanar cutar saboda irin lunguna, ofisoshi da kuma irin mutanen da muke ganawa da su.

“Wasu mutane za su ba ka hannu ku yi musabaha idan ka ki karba sai su nuna basu ji dadi ba.” Inji Sani.