’Yan kabilar Eggon sun yi alkawarin tauye Labaran Maku a zaben 2015

kungiyar masu ruwa da tsaki ta ’yan kabilar Eggon a Jihar Nasarawa ta bayyana Sanata Solomon Ewuga a matsayin wanda za ta mara wa baya ya tsaya takarar Gwamnan Jihar. Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma tsohon shugaban karamar Hukumar Nasarawa Eggon, Mista Dogara Angbo ya rattaba wa […]

’Yan kabilar Eggon sun yi alkawarin tauye Labaran Maku a zaben 2015
’Yan kabilar Eggon sun yi alkawarin tauye Labaran Maku a zaben 2015

kungiyar masu ruwa da tsaki ta ’yan kabilar Eggon a Jihar Nasarawa ta bayyana Sanata Solomon Ewuga a matsayin wanda za ta mara wa baya ya tsaya takarar Gwamnan Jihar. Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma tsohon shugaban karamar Hukumar Nasarawa Eggon, Mista Dogara Angbo ya rattaba wa hannu aka raba wa manema labarai a Lafiya ranar Litinin. Sanarwar ta ce bayan zama na musamman da shugabannin kungiyar suka yi kasancewa wasu jiga-jigan ’yan siyasa daga kabilar su 4 suna sha’awar tsayawa takarar, ta zabi Sanata Solomon Ewuga ne daga cikin su Ministan Labarai Mista Labaran Maku daga Jam’iyyar PDP da Mista Mathew Ombugaku daga APGA da Dokta James Angbazo daga Jam’iyyar APC, saboda la’akari da farin jini da gudunmawar da Sanata Ewuga ke bayarwa ga ci gaban kabilar da jihar baki daya.
Sai ta shawarci sauran ’yan kabilar da ke niyyar fito takarar Gwamnan musamman Ministan Labarai Labaran Maku da kada ya ba kansa wahala cewa zai fito takarar, saboda kada ya yi biyu-babu, domin a cewarta ba zai samu goyon bayan ’yan kabilar Eggon ba.
kungiyar ta ce za ta wulakanta shi idan ya ki bin wannan shawara ta hanyar kin kada masa kuri’a a lokacin zaben.
Shugaban kungiyar Matasa masu son tabbatar da nasarar Sanata Ewuga a zaben Gwamnan, Mista Jilemsam Abel Sama’ila ya bayyana Sanata Ewuga ya bukaci sauran masu sha’awar tsayawa takarar su hada hannu da Sanatan don tabbatar ya samu nasara maimakon su fito takara su yi asara, domin al’ummar Eggon da wadanda ba Eggon ba a jihar suna bayan Sanata Ewuga ne.