’Yan kabilar Ibo ina kuka dosa?
“Jamhuriyar kasar nan, wadansu tsirarin kabilu da ake kira Fulani, wadanda ba su taba boye niyyarsu ba ta su kakkabe sauran ’yan kasa da addinansu da zimmar mayar da kasar, kasar Musulmi, kamar yadda a jahilce Kungiyar Fulani ta Kasa (FUMAN) ta yi ikirari.” Wadannan kalamai da makamantansu na tada fitina, na cikin kalaman sanarwar […]
“Jamhuriyar kasar nan, wadansu tsirarin kabilu da ake kira Fulani, wadanda ba su taba boye niyyarsu ba ta su kakkabe sauran ’yan kasa da addinansu da zimmar mayar da kasar, kasar Musulmi, kamar yadda a jahilce Kungiyar Fulani ta Kasa (FUMAN) ta yi ikirari.” Wadannan kalamai da makamantansu na tada fitina, na cikin kalaman sanarwar bayan wani hadadden taro na kasa kuma irinsa na farko da shugabannin kungiyoyin kabilar Ibo suka fitar a Owerri babban birnin Jihar Imo a karshen watan Agustan bana, suka kuma kira a “Matsayi ko Ikirarin Owerri.” Taron da Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Enugu, Jakada Lawrence Agubuzu ya shugabanta.
Sanarwar bayan taron mai taken: “Zaman lafiya da tsaro da ci gaban Alaigbo da makwabtansu da shugabannin kungiyoyi irin Gidauniyar Ci gaban Alaibo da makwabtansu Farfesa Uzodimma Nwala da Shugaban Kwamitin Shirya Taron Farfesa Ukachukwu Awuzie da Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Gari-Gari na Shiyyar Kudu maso Gabas, Mista Emeka Diwe da wadansu shugabannin kungiyoyi kabilar Ibo daban-daban har 21 suka sanya wa hannu, ta yi la’akari da irin yadda wai ake ta danne ’yan kabilar Ibo, ta hanyar mayar da su saniyar ware a dukkan harkokin tafiyar da kasar nan, al’amarin da ya kai matsayin duk wani gwaggwaban mukami yana hannun ’yan Arewa.
Wannan, inji mahalarta taron, ya sanya yanzu kasar nan ta zama wata ta daban, a kan makomar siyasa, ta yadda hakan ya sa ta rasa muhimman manufofi a kan doka da oda, adalci da samun daidaito da girmama juna a tsakanin ’yan kasa, ta yadda kowa ke yin abin da ya ga dama tamkar babu gwamnati. Sun kuma yi la’akari da cewa annobar rashin zaman lafiya da kasar nan take fama da shi ta samo asali ne daga hadakar da aka yi, da tun farko babu sanin darajar juna, balle girmamawa, al’amarin kuma ya kara ta’azzara da gangan ko da ganganci, Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya suka dauki mulkin kasar nan suka mika ga al’ummar Fulani ’yan tsirarun kabilu, tun farkon samun ’yancin kan kasar nan.
A zaman mafita ga ’yan kabilar Ibo, sanarwar bayan taron, ta nemi lallai dukkan kungiyoyin kabilar Ibo na ciki da wajen kasar nan da suka hada da Gidauniyar Ci gaban Alaigbo da na Gamayyar Kungiyoyin Gari-Gari na Kudu maso Gabas da Majalisar Kabilar Ibo ta Duniya da dukkan malaman addinin Kirista, musamman na kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) shiyyar Kudu maso Gabas, kai har ma da haramtacciyar Kungiyar Tabbatar da Kasar Biyafara (IPOB), su hada karfi da karfe wajen mikewa tsaye don tabbatar da makomarsu a kasar nan, kasancewarsu mutanen da suke dunkule kuma masu son zaman lafiya da ci gaban rayuwarsu.
Ga mahukunta da sauran ’yan kasa baki daya kuma mahalarta taron na ’yan kabilar Ibo, kira suka yi a gaggauta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin ’yan kasa baki daya da za ta tantance makomar ’yan kabilar Ibo na kasar nan da shiyyarsu ta Kudu maso Gabas. Shiyyar da ta kunshi jihohin Enugu da Anambra da Imo da Abiya da Ebonyi.
Duk tsawon mulkin tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasonjo na shekara takwas a Jam’iyyar PDP (1999 zuwa 2007), ’yan kabilar Ibo suke rike da mukami na uku, a kasar nan, wato na Shugaban Majalisar Dattawa kamar haka: Sanata Chuba Okadigbo 1999 zuwa 2000, sai tsakanin 2000 zuwa 2003, Sanata Pius Ayim Pius ya gaje shi, Sanata Adolphus Wabara ya dana shugabancin Majalisar Dattawan tsakanin shekarar 2003 zuwa 2005, yayin da Sanata Ken Nnamani ya karba a shekarar 2005, ya karkare da shugaba Obasonjo a shekarar 2007.
Ai, koda da tsarin karba-karba na Jam’iyyar PDP da ya sa mulki dawowa Arewa a shekarar 2007, da marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa ya gaji Cif Obasonjo, Dokta Goodluck Ebele Jonathan daga Jihar Bayelsa a shiyyar Kudu maso Kudu, ya kasance Mataimakinsa, Dokta Goodluck da ya sha ikirarin cewa shi Ibo ne kuma babu wani shugaban kungiyar kabilar Ibo da ya taba karyata ikirarinsa.
A duk tsawon mulkin marigayi ’Yar’aduwa na shekara uku da wanda shugaba Jonathan ya yi na shekara biyar, babu wani lokaci da wani ko wadansu shugabannin kabilar Ibo a cikin gida da wajen kasar nan da aka taba jin yana kokawa da an danne su ko ba a yi da su, ballanta a ji hayaniyar za su balle kamar yadda suke tunda Shugaba Buhari ya zo kan karagar mulki a shekarar 2015.
Maganar da ake dai yanzu a dukkan jihohin kabilar Ibon biyar, ba inda Jam’iyyar APC take da Gwamna, duk Jam’iyyar PDP ke mulki a jihohin. Hatta a Jihar Imo da a zaben shekarar 2015, Gwamnan Jihar Mista Rochas Okorocha ya bar jam’iyyarsu ta APGA ya koma Jam’iyyar APC ya kuma ci zabe a inuwarta karo na biyu, amma sai ga shi a zaben bana saboda rikicin siyasar da ya auka wa jihar kafin zaben dan takarar da ya tsayar na neman Gwamnan Jihar a wata jam’iyyar bai kai ga nasara ba, duk kuwa da Cif Rochas ya samu nasarar lashe zaben dan Majalisar Dattawa a inuwar Jam’iyyar APC din. Abin tambaya shi ne ta ina kabilar Ibo za su samu shugabancin kasar nan a shekarar 2023? Suna jin hargowa da tada husuma da tarzoma da cin mutunci ko bata sunan masu mutunci ’yan Arewa, musamman Shugaban Kasa Buhari zai sa a dauki mulki a ba su?
A irin wannan hali ne wani dan kabilar Ibo Dattijo Cif Mbazulike Amechi dan shekara 92, kuma daya daga cikin ’yan gani-kashe-nin tafiyar siyasar tsohon Shugaban Kasar nan a Jamhuriya ta Daya, Dokta Nnamdi Azikwe, a Jam’iyyar NCNC, a kwanakin baya ya tambayi ’yan uwan nasa kamar haka: “Wai don me ’yan kabilar Ibo suke son su kutsa kai, su kuma zama cikin na gaba-gaba a gwamnatin APC da ba su yi wa aikin komai ba?” Ya ci gaba da cewa “Bai kamata ba a wannan lokaci ’yan kabilar Ibo su rika hankoro da barazanrar sai an ba su mukamai a wannan gwamnati, maimakon haka ya kamata su kara daura damara da tuntuba da tattaunawa a kan yadda dan kabilar Ibo zai zama Shugaban Kasa a shekarar 2023.” Illa iyaka inji Cif Amechi.
Shi ma tsohon dan siyasar nan tun a Jamhuriya ta Farko a inuwar Jam’iyyar NEPU SAWABA, Alhaji Tanko Yakasai, tunatar da ’yan kabilar Ibon ya yi cewa barazanar za su balle da tozartawa da suke yi wa Shugaba Buhari da mutanen Arewa ba za su sa a dauki mulki a ba su a bagas ba. Wadannan ra’ayoyi biyu haka suke. Ya kamata ’yan kabilar Ibo su kwana da sanin cewa bisa ga zargin da ake wa wasunsu na shahara a kan aikata miyagun ayyukan irin na safarar miyagun kwayoyi da fashi da makami da sauran ayyukan zamba a ciki da wajen kasar nan da suke batawa da cutar da akasarin matasa musamman na Arewa da na kasar nan baki daya, da ma a kasashen ketare, ya kamata su sani cewa mafi yawan ’yan Arewa za su yi murna idan aka ce yau ’yan kabilar Ibo sun samu kasarsu ta kansu.