’Yan kabilar Ibo sun kai gwamnatin Legas kotu suna neman diyyar Naira biliyan daya

’Yan kabilar Ibo 76 da gwamnatin Jihar Legas ta kwasa ta kai Anaca ta jibge bayan tsare su a  wurare daban-daban kafin kai su Anaca sun kai karar gwamnatin kotu suna neman a biya su diyyar Naira biliyan daya a kan abin da suka kira take hakkin su da gwamnatin ta yi.Mutum bakwai daga cikin […]

’Yan kabilar Ibo sun kai gwamnatin Legas kotu suna neman diyyar Naira biliyan daya
’Yan kabilar Ibo sun kai gwamnatin Legas kotu suna neman diyyar Naira biliyan daya

’Yan kabilar Ibo 76 da gwamnatin Jihar Legas ta kwasa ta kai Anaca ta jibge bayan tsare su a  wurare daban-daban kafin kai su Anaca sun kai karar gwamnatin kotu suna neman a biya su diyyar Naira biliyan daya a kan abin da suka kira take hakkin su da gwamnatin ta yi.
Mutum bakwai daga cikin 76 ne suka shigar da karar a Babban Kotun Legas, inda baya ga kudin da suka nema, sun kuma nemi gwamnatin jihar ta rubuta takardar ban hakuri a wasu fitattun jaridun Najeriya na tsawon wata daya.
Har wa yau sun bukaci kotu ta sa gwamnatin ta samar musu muhalli a cikin sakamakon take musu hakkinsu da ta yi. Sun ce an kama su an tsare na tsawon kwanaki ba tare da bayyana musu laifin da suka yi ba, kuma ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba. Sun ce a matsayinsu na ’yan Najeriya suna da ikon zama a kowane sashi na kasar nan kamar yadda tsarin mulki ya nuna.
Tun kafin su je kotu Gwamnan Jihar Legas Mista Babatunde Raji Fashola ya roki gafarar wadanda al’amarin ya shafa, kuma kamar sun hakura kwatsam sai ga sammaci an aika wa gwamnatin jihar.
Gwamnan ya fadi a lokacin ba su hakuri a wani taro da ’yan kabilar Ibo da a Legas cewa: “Ga wadanda ba su fahimtar manufar gwamnatinmu su ke ganin mun yi musu ba daidai ba, yau zan yi amfani da wannan damar domin ba ku hakuri.”
Alkalin kotun Mai shari’a Ajugomobia ya ajiye wata Janairun badi domin fara sauraron shari’ar.
Kwashe mutane a raba su da Jihar Legas ba wannan ne irinsa na farko da jihar ta yi ga ’yan asalin wasu jihohi ba, musamman wadanda suka fito daga Arewa, wadanda suka fi fuskantar wannan tozartawa, amma ba wani daga cikin fitattun Arewa da ya taba fitowa ya soki wannan tursasawa da ake yi wa ’yan uwansu.