’Yan Kalare: ‘Da haɗin kan jama’a za mu magance rashin tsaro’
Al’ummar Gombe sun yi wa kwamishinan ’yan sanda takakkiya domin ganin an kawo ƙarshen ayyukan ’yan dan Kalare
Shugabannin al’ummar unguwannin Barunde da Manawachi da ke Gombe sun nemi tallafin ’yan sanda domin kawo ƙarshen matsalar ’yan Kalare da rikicin ’yan daban a yankunansu.
Shugabannin yankunan su haɗa kai tare da neman ɗaukin ’yan sanda ne a sakamakon yawaitar ayyukan ’yan Kalare a unguwannin waɗanda ke maƙwabtaka da juna.
Sun bayyana haka ne a lokacin da suka ziyarci Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, CP Hayatu Usman, inda suka miƙa ƙoƙon baransu.
A ci gaba da kokarin kawo ƙarshen ayyukan ’yan daba da masu aikata laifuka, musamman ’yan Kalare, Kwamishinan ’Yan Sandan ya jagoranci zama na musamman tare shugabannin tsaro na yankunan.
- Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda
- Lakurawa sun tsere bayan sojoji sun ragargaje su a Kebbi
Taron ya samu halartar shugabannin al’umma da na addini da ’yan kwamitin tsaro daga unguwannin, har ma da DPO na unguwar Low Cost, CSP Usman Muhammad.
A jawabin CP Usman, ya jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan al’umma ga ’yan sanda domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan daba, musamman ’yan Kalare da suka addabi yankunan.
Kwamishinan ya kuma yi wa al’ummar Barunde ta’aziyya bisa kisan matashin nan, Bashar Idris, mai shekara 29, wanda ya rasa ransa a rikicin ’yan Kalare daga yankin Manawachi.
Ya tabbatar wa al’ummar cewa rundunar za ta ɗauki matakan gaggawa domin ganin an kama waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki.