’Yan Kalaren Bolari Sun Ajiye Makamai
Ana rarrashinsu ne ba don sun fi karfi hukuma, sai dai ana so su zaman mutanen kirki.
Gagararrun matasa da ke dabanci wadanda aka kira ’yan kalare a unguwar Bolari ta Jihar Gombe sun yi sulhu da juna tare da ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya.
Kwamandan hukumar tsaro ta sibil difens na Jihar Gombe tare da hadin guiwar Dattawa da Hakimin Bolari ne suka jagoranci sulhun da kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin matasan.
- NAJERIYA A YAU: Me Doka Ta Ce Idan Mutum Bai Iya Rera Taken Najeriya Ba?
- Mutum biyu sun binne ɗan uwansu da ransa a Zariya
Wakilinmu ya ruwaito cewa, matasan dai sun yi kaurin suna wajen haddasa tashe-tashen hankali, da kwacen wayoyi da rana tsaka kuma babu mai tanka musu har su kwana lafiya a gidajen iyayensu.
Sai dai a yayin sulhun, an tara matasan ne a Fadar Hakimin Bolari Malam Ahmed Abubakar, inda suka yi alkawarin sun tuba sun ajiye makamai kuma sun yarda su zauna lafiya da kowa babu fada.
A jawabinsa ga matasan, Hakimin Bolari Ahmed Abubakar Bolari, ya ce wannan shi ne karo na hudu da Kwamandan Sibil difens ya ke zuwa Fadar Bolari don ganin ya sulhunta matasan sun zama mutane nagari domin sun addabi jama’a.
Ya ce shi ma a matsayinsa na Sarki ya yi zama da wasu daga cikin iyayen yaran don ganin cewa an yi wa tufkar hanci sun daina sara-suka da suke yi wa junansu da kwacen kayan mutane, amma ba a samu nasara ba sai a wannan lokaci.
Ya bayyana cewa ta’addancin da suke yi ya bata sunan unguwar Bolari, amma yanzu tunda sun ajiye makamai yana son darajar unguwar ta karu a idon jama’a
A nasa bangaren, Kwamandan na Sibil Difens, Muhammad Bello Mu’azu, jan hankalin su ya yi da cewa idan suka tabbatar ba za su sake daukar makami ba ya yi alkawarin mayar da masu sha’awar karatu a cikinsu makaranta, sannan masu son sana’a kuma zai yi magana da gwamnati ta samar musu da abun yi.
Ya ce ana rarrashinsu ne ba don sun fi karfi hukuma, sai dai ana so su zaman mutanen kirki wanda nan gaba da za su taimaki kansu su taimaki al’umma domin ba wanda zai so a ce dansa ya lalace balle dan wani.
Shi ma Malam Abubakar Bolari, daya daga cikin dattawa da yake ta fadi-tashi wajen ganin matasan sun shiryu, ya yi musu gargadi da nasiha sosai na rashin kyawun abin da suke aikatawa
Abubakar Bolari, ya ce kafin wannan rana ta sulhu, babu wanda bai je har gidajen iyayensu , inda kuma duk sun nuna masa rashin jin dadin su na lalacewar tarbiyar ’ya’yansu.
Malam Bola ya kuma ja musu kunne dangane da muhimmancin rike alkawarin da suka dauka a yanzu na rungumar zaman lafiya da watsi da makamai
Aminiya ta ruwaito cewa, matasan da suka zo taron sulhun sun mika wa Kwamandan na sibil difens makamansu, inda shi kuma ya mika wa Hakimin Bolari domin ta tabbatar sun ajiye makamai fada ya kare.
Wasu daga cikinsu da muka zanta dasu sun tabbatar da cewa za su zauna lafiya da juna tunda unguwarsu daya daga yanzu fada ya kare.