’Yan KAROTA sun haddasa hadari a Kano
A ranar Litinin da ta gabata wasu jami’an sabuwar hukumar nan mai kula da ayyukan da suka shafi hanya da aka fi sani da KAROTA suka haddasa hadari a Unguwar Mariri inda mutum daya ya rasu mutum uku ciki har da yaro mai kimanin shekara biyu suka samu raunuka.Aminiya ta samu bayanin cewa bayan aukuwar […]

A ranar Litinin da ta gabata wasu jami’an sabuwar hukumar nan mai kula da ayyukan da suka shafi hanya da aka fi sani da KAROTA suka haddasa hadari a Unguwar Mariri inda mutum daya ya rasu mutum uku ciki har da yaro mai kimanin shekara biyu suka samu raunuka.
Aminiya ta samu bayanin cewa bayan aukuwar hadarin matasan unguwar sun yi zanga-zangar kan ayyukan hukumar inda suka nufi ofishin hukumar da ke Club Road.
Wani ganau mai suna Amadu Mairake Mariri ya ce lamarin ya auku ne da karfe goma saura kwata na safe lokacin da wani jami’in KAROTA ya yi yunkurin kama wata motar haya kirar Golf mai dauke da fasinjoji 8 da ta nufi Jihar Jigawa.
Ya kara da cewa ganin sun tsayar da direban ya ki tsayawa sai jami’an KAROTA suka bi motar a guje, hakan ya sa motar ta kauce daga hanyya ta kara wa bishiya mutum daya ya rasu da dama suka samu rauni.
Wani ganau da ya nemi a saya sunansa ya shaida wa Amniya cewa dama ’yan KAROTA sun addabi jama’a, saboda haka da mutanen Unguwar Mariri suka fahimci cewa jami’an KAROTA sun gudu bayan aukuwar hadarin sai suka harzuka suka datse hanyar Kano zuwa Maiduguri. “A kullum sai ka ji an ce ga abin Allah wadai da ‘yan KAROTA suka yi, na dauka surutun jama’a ne don a kassara kokarin gwamnati. Sai dai abin da ya faru jiya (Litinin) ya tabbatar da cewa jami’an KAROTA suna bukatar a bi diddigin ayyukansu. Ta yaya za a ce ku bi mota a guje a kan babban titi don kuna son kama ta, sannan ku gudu bayan kun haddasa hadari?,” inji shi.
An kai wadanda suka samu rauni Asibitin Murtala da ke Kano, kuma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun gana da shugabannin KAROTA a kan lamarin, kuma jami’an hukumar guda hudu suna hannun ’yan sanda. Ya ce suna gudanar da bincike kuma za su dauki matakin da ya kamata bayan kammala binciken.
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Shugaban Hukumar KAROTA Alhaji Muhammad Gambo Diggol ya ci tura, kasancewar ya ki amsa wayar da aka yi masa haka kuma bai bayar da amsar sakon tes da aka aika masa ba.