’Yan kasuwa a Karmo sun tafka asara sakamakon gobara

Wata gobara da ta fara da misalin karfe daya na daren Larabar makon jiya ta yi sanadiyyar salwantar miliyoyin Naira bayan ta cinye shaguna da adadinsu ya kai 340 a kasuwar Karmo da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja. Gobarar wadda ake kyautata zaton ta auku ne a sakamakon tsinkewar babbar wayar lantarki da ta […]

’Yan kasuwa a Karmo sun tafka asara sakamakon gobara

Wata gobara da ta fara da misalin karfe daya na daren Larabar makon jiya ta yi sanadiyyar salwantar miliyoyin Naira bayan ta cinye shaguna da adadinsu ya kai 340 a kasuwar Karmo da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Gobarar wadda ake kyautata zaton ta auku ne a sakamakon tsinkewar babbar wayar lantarki da ta ratsa ta kasuwar, wadda ta wucin-gadi ce ta kuma rutsa da wasu gidaje biyu da ke hade da kasuwar, kafin aka samu nasarar cin karfinta da misalin karfe goma na safiyar Alhamis.

Wani wanda lamarin ya shafa mai suna Alhaji Kabiru kwara da ya rasa shaguna 2 na kayan abinci da dakin ajiya na shinkafa daya da kuma na kayan wutar lantarki, ya ce gobarar ta shafi layukan sayar da kayan abinci na kasuwar da na masarufi da kuma na yadi, wadanda su ne cibiyar hada-hadar kasuwar, sai kuma wasu shaguna na sayar da wayar sadarwa da na kayan lemo da kuma na kwalliyar mata.

Sakataren kasuwar, Malam Yusuf kani ya bayyana wa Aminiya cewa bayan masu tsaron kasuwar sun ankarar da su a kan lamarin, sun kula da wayar wutar da ta fado a kan shagon, inda nan ne wutar ta fara ci. Ya ce bayan sun yi yunkurin kashe wutar ba tare da nasara ba, sun garzaya babban ofishin ’yan sanda na garin, inda suka yi kamar awa guda kafin hukumar kashe gobara ta dau waya. “Sai dai ko da suka iso kasuwar sai suka kula motarsu ba ta da ruwa sannan suka koma. Wutar ta yi ta barna ba tare da mun iya yin komi ba, in banda zuba wa sarautar Allah ido.

“Sai da misalin karfe 4 na dare ne su ka samu dawowa, sai dai kasancewar ana sanyi da iska wutar ta yi ta bunkasa cikin hanzari kafin isowarsu. Daga baya ne wasu karin motoci daga Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA) da kuma rundunar sojan sama da na ruwa su ma suka kawo dauki kafin a samu nasarar kashe wutar da misalin karfe goma na safe,” inji Sakataren kasuwar.

Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello da Shugaban karamar Hukumar Birni Da Kewaye na Abuja, Malam Abdullahi Adamu Kandido da Sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa sun kai ziyarar jajantawa ga ’yan kasuwar tun a ranar da matsalar ta auku, inda Ministan ya yi alkawarin tallafa masu.

Wani da matsalar ta shafa a kasuwar mai suna Malam Musa Shukra, ya ce sai dai tuni ’yan kasuwar suka fara share rumfunarsu tare da kasa kaya a filin Allah, inda kuma suke dakon taimako daga bangaren gwamnatin.