’Yan kasuwa da dalibai sun nuna goyon bayansu ga gwamnatin Oyo
A yayin da aka kasa cin ma matsaya a zaman sulhu da aka yi a tsakanin Gwamnatin Jihar Oyo da kungiyar kwadago (NLC) da ’ya’yanta suke yajin aiki a jihar, su kuwa ’yan kasuwa da dalibai da jama’ar gari fitowa suka yi kwai da kwarkwata nsu suka yi jerin gwano a birnin Ibadan, a ranar […]
A yayin da aka kasa cin ma matsaya a zaman sulhu da aka yi a tsakanin Gwamnatin Jihar Oyo da kungiyar kwadago (NLC) da ’ya’yanta suke yajin aiki a jihar, su kuwa ’yan kasuwa da dalibai da jama’ar gari fitowa suka yi kwai da kwarkwata nsu suka yi jerin gwano a birnin Ibadan, a ranar Litinin da ta gabata domin nuna amincewa da irin salon mulki da Gwamna Abiola Ajimobi yake yi. Wannan ita ce zanga-zangar hadin gkiwa a tsakanin kungiyoyi daban-daban da ta fi tara mutane masu yawa domin goyon bayan salon mulki a jihar.
dinbin mutane maza da mata da suka yi wannan zanga-zangar lumana sun taru ne a babban zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin Ibadan, daga nan suka fara yin doguwar tafiya a kasa suna rera wakokin yabon gwamnati har suka isa ofishin Gwamna da ke Agodi. ’Yan sanda dauke da bindigogi da motocin sulke ne suka yi wa masu zanga-zangar kariya na tsawon yinin wannan rana.
Cikin jawabinsa ga dimbin masu zanga-zangar, Gwamna Abiola Ajimobi ya nuna matukar farin cikinsa da yadda kungiyoyin suka tsara doguwar tafiyar da suka yi a kasa ba tare da samun wata matsala a kan hanyoyi ba. Ya ce: “Lallai ne kun tabbata da kishin ci gaban Jihar Oyo da kasa baki daya, domin kun fito ku nuna kyamarku ga yunkurin kawo cikas ga ayyukan ci gaban jiharku ne. Abun da kuka yi goyon baya ne ga tsarin dimukuradiyya da alkawarin da muka yi a lokacin da muka karbi jagoranci a karo na biyu. Zaman tattaunawar wata matsala a tsakanin mutane biyu masu jayayya, makami ne na lalubo hanyar dinke baraka da aza tubalin ginin gidan karfe.”
Da yake magana dangane da batun mayar da makarantun sakandare ga hannun kungiyoyi masu zaman kansu, Gwamnan ya sake tabbatar da nufinsa na samar da hanyoyin bunkasa ilmi ne amma ba ya da nufin kada kararrawar gwanjatar da makarantun ko sayar da su kamar yadda makiyan gwamnati suke baza jita-jita domin durkusar da ci gaban ilmi da cin ma burinsu.
“Na umarci dukkanku idan kun koma wuraren da kuka fito, ku isar da sakona ya bazu ga jama’a cewa, babu wani nufi da gwamnati ta yi domin sayar da makarantun sakandare ga wasu mutane. Ina yin kira gare su da su girmama tattaunawar zama bisa teburi daya domin muna bukatar su zo mu zauna domin shawo kan wannan matsala, domin babu abun da zai haifar da takaddama a tsakaninmu da kungiyar kwadago da ta umarci ma’aikata da yin yajin aiki.” Inji Gwamnan, wanda ya ci gaba da cewa: “Babu wata matsala a tsakaninmu da su, sai dai kawai wasu daga cikinsu da suke yin amfani da siyasa domin lalata al’amari.”
Wakilan kungiyoyi daban-daban ne suka yi jawaban nuna goyon baya ga salon mulkin gwamnati a Jihar Oyo da sun yi alkawarin za su ci gaba da goyon bayan tsarin mayar da makarantun sakandare da gwamnati ta ce za ta fara a cikin watan Satumba mai zuwa.