‘Yan kasuwa na bukatar dauki daga gwamnati – Iliyasu Muhammad

Wani dan kasuwa kuma shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta Jihar Filato, Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo dauki ga harkokin kasuwanci a kasar nan. Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.  Ya ce gwamnati ta kawo dauki ga harkokin […]

‘Yan kasuwa na bukatar dauki daga gwamnati – Iliyasu Muhammad

Wani dan kasuwa kuma shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta Jihar Filato, Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo dauki ga harkokin kasuwanci a kasar nan. Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. 

Ya ce gwamnati ta kawo dauki ga harkokin kasuwanci a kasar nan ya zama wajibi, domin yanzu harkokin kasuwanci yana cikin wani mawuyacin hali a Najeriya. Ya ce  yanzu ‘yan kasuwa suna cikin wani mawuyacin hali a Najeriya, sakamakon rashin ciniki.

‘Rashin kudi a hanun jama’a da rashin biyan albashin ma’aikata ne ya kawo wannan al’amari. Mafita kan wannan al’amari shi ne gwamnati ta tallafawa kamfanoni manya da kanana da ‘yan kwangila kuma  gwamnatocin jihohi su rika biyan albashi da ayyukan raya kasa’’. 

 

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna