‘Yan kasuwa sun bayyana amfanin kudin tallafin TraderMoni

Yan kasuwa daban-daban da suka samu tallafin kudin kasuwanci na tsarin Tradermoni sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana irin amfanin da za su samu daga tsarin. Dan kasuwa mai suna Abubakar Zaki da ke sana’ar sayar da tumatir a rumfarsa da ke kasuwar Utako a Abuja da wakilinmu ya ziyarci wajen sana’arsa, an tambaye […]

‘Yan kasuwa sun bayyana amfanin kudin tallafin TraderMoni

Abubakar Zaki, mai sayar da tumatir a kasuwar Utako ya samu rancen kuxin Tradermoni

Yan kasuwa daban-daban da suka samu tallafin kudin kasuwanci na tsarin Tradermoni sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana irin amfanin da za su samu daga tsarin.

Dan kasuwa mai suna Abubakar Zaki da ke sana’ar sayar da tumatir a rumfarsa da ke kasuwar Utako a Abuja da wakilinmu ya ziyarci wajen sana’arsa, an tambaye shi cewa, ko ya samu kudin tallafi na kananan ‘yan kasuwa Tradermoni da gwamnati take bayarwa?

Sai ya amsa cikin gaggawa  cewa, Eh na samu kudin tallafin kudin kananan ‘yan kasuwa na Tradermoni. Ina kara sayan tummatir da attarugu da nake sayarwa kudin da aka bani ya taimaka min sosai. Amma a yanzu haka idan na samu karin kudi da yakai naira dubu 50 rumfa ta zata sake bunkasa, kudin da aka bani basu isheni ba, ina fatan zan iya biyan bashi, in ji Zaki.

Wanda ke makwabtaka da rumfar Zaki, mai suna Isah Musa wanda yake sayar da doya da albasa. Musa ya ce, na samu tallafin kudin gwamnatin tarayya na naira dubu 10. Na gode wa Allah da yasa na samu naira dubu 10 inda na samu na kara jarin kasuwancinsa.Ina bukatar karin kudi ko nawa ne, zan yi murna sosai. Sai dai gashi jama’a da dama basu samu kudin tallafin ba. Amma ina fatan wasu ma su samu, saboda samun kudin zai tallafawa kananan ‘yan kasuwa kamar mu.

Wani dan kasuwa mai suna Salisu Shehu mai sana’ar tireda ya ce, “ya yi rijistar samun tallafin kudin amma har yanzu bai samu sakon shigar kudin rancen ba, saboda ina bukatar gwamnati ta tallafa min da kudin”.

Wani mahauci a kasuwar Nyanya Mallam Salisu Ibrahim, ya ce, ya yi  rijistar neman kudin rancen amma har yanzu bai samu kudin ba. Mai sana’ar sayar da naman ya ce, darajar kudin naira ya ragu ba kamar yadda yake ada ba. Ya kara da cewa, kudin zai iya sa a sayi akuya ba tare da sayan naman saniya ba don sayar wa. Don haka yake bukatar kudin wanda hakan zai kara masa yawan jarin kasuwancnsa.  Kuma ya bayyana cewa, ya nada yakinin mahauta zasu iya biyan kudin rancen da suka karba, ba tare  da wata matsala ba.

Wata mai sayar da abinci Grace Olofu, ta bayyana wa majiyarmu cewa, kudi zai taimaka  mata wajen sayar da abinci masu yawa.

Ta ce, wani lokaci ta sayar da abincin ne ta hanyar bashi bayan ta sayar sai ta biya bashin.

Gwamnatin tarayya ta kirkiro da shirin bayar da rance ga kananan masana’antu ‘Micro Small and Medium Enterprises (MSME)’ don bunkasa tattalin arzikin kasar.

A kwanakin baya ne mataimakin shugaban Najeriya ya kaddamar da shirin bayar da rancen kudi a kasuwar Utako da ke Abuja, shirin na yunkurin tallafawa kananan ‘yan kasuwa miliyan biyu a duk fadan kasar akan kowanne dan kasuwa ya samu naira dubu 10 bayan  wata uku zuwa shida ya biya.

Shirin kawai na kananan ‘yan kasuwa ne wanda hakan zai taimaka wa jarinsu ya bunkasa.