’Yan kasuwa sun fara yajin aiki kan karin kudin mai a Pakistan

’Yan kasuwa sun fara yajin aiki sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da na haraji a kasar Pakistan da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki.

’Yan kasuwa sun fara yajin aiki kan karin kudin mai a Pakistan

Shugaban da aka rufe a wata kasuwa da ke birnin Karachi da ke kasar Pakistan. (Hoto: Rizwan Tabassum/AFP)

’Yan kasuwa sun fara yajin aiki sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da na haraji a kasar Pakistan da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki.

An rufe kasuwanni da dama a ranar Asabar a biranen Lahore, Karachi da Peshawar inda suka sanya allunan da ke kokawa bisa “karin karin kudin wutar lantarki da na haraji da bai dace ba”.

Gwamnatin ta yi karin farashin tare da janye tallafi ne bisa bukatar Asusun Lamun na Duniya (IMF) da ke bin ta bashi, domin guje wa gaza biyan bashin da gwamnatin ta ciyo daga kasashen waje.

shugaban kungiyar ’yan kasuwa ta birnin Lahore, Ajmal Hashmi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, “Kowa yana shiga yajin aikin saboda halin da muke ciki a yanzu ba wanda ba za a iya jurewa ba ne.

“Dole ne a ba da wasu tallafi domin mutane su iya samun abin da da zau kai wa bakin salati.”

’Yan kasuwa dai na da karfin fada-a-ji da kuma tasiri sosai a kasar ta Pakistan da ke shirin gudanar da babban zabe cikin watanni masu zuwa.

Hakan ya sa ake ganin yanzu gwamnatin kasar na da jan aiki a gabanta na yin yadda ’yan kasuwar suke so ta cire karin farashin, ko kuma ta yi abin da IMF ke so.

Pakistan dai ta sha fama da karancin haraji — ciki har da ‘yan kasuwa — wadanda ake ganin sun ja ta tara dimbin basussukan kasashen waje da take kokarin ragewa.