‘Yan kasuwa sun kai Jang kara kan yunkurin rusa kasuwar Abuja market

’Yan kasuwar Abuja market da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun kai Gwamnan jihar  Jonah Jang da gwamnatin jihar da hukumar bunkasa garin Jos da kewaye [JMDB]  kara a Babbar Kotu a Jos,  kan yunkurin rusa shagunan kasuwarsu. ’Yan kasuwar sun shigar da karar ne a Larabar makon jiya don kotu ta hana […]

‘Yan kasuwa sun kai Jang kara kan yunkurin rusa kasuwar Abuja market
‘Yan kasuwa sun kai Jang kara kan yunkurin rusa kasuwar Abuja market

’Yan kasuwar Abuja market da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato sun kai Gwamnan jihar  Jonah Jang da gwamnatin jihar da hukumar bunkasa garin Jos da kewaye [JMDB]  kara a Babbar Kotu a Jos,  kan yunkurin rusa shagunan kasuwarsu.
’Yan kasuwar sun shigar da karar ne a Larabar makon jiya don kotu ta hana rushe kasuwar da gwamnatin jihar take yunkurin yi.
Idan ba a manta ba a watan Mayun da ya gabata ne aka kai harin bama-bamai a  kusa da kasuwar,  wanda  ya janyo asarar rayuka da  dukiyoyi masu tarin yawa.
Alhaji Sabo Adamu da wasu mutane 11 sun shigar da karar ne  a gaban Mai shari’a P.L. Lot na babbar kotu ta 4 da ke Jos, inda suka ce yunkurin da hukumar bunkasa garin Jos da kewaye [JMDB] ke yi na rusa kasuwar ya saba yarjejeniyar da ta kulla da ‘yan kasuwar.
’Yan kasuwar sun bukaci kotun ta sanya wadanda ake karar su bude babbar  kasuwar Jos da kasuwar Abuja market da kasuwar Railway da ta ‘yan haya ba tare da sanya wani sharadi ba.
Sun bukaci kotun ta sanya wadanda ake karar su biya ‘yan kasuwar diyyar Naira miliyan 500 sakamakon mawuyacin halin da suka shiga da kuma asarar da suka yi bayan an rufe wannan kasuwa.
Gwamnatin jihar ta Filato dai na shirin rusa kasuwar ne saboda a cewar ta, ginin kasuwar ba shi da nagartar da mutane za su iya zama a ciki, sakamakon girgiza shi bama-bamai suka yi tun bayan harin watan Mayu da aka kai kusa da kasuwar.
A makon jiya Janar-Manajan Hukumar bunkasa birnin Jos da kewaye [JMDB] Birgediya Janar Musa Gambo ya ba  ’yan kasuwar umarnin kwashe kayayyakinsu, don a aiwatar da aikin rushe kasuwar.