’Yan kasuwa sun kai wa masarautar Agege ziyara
A kwanakin baya ne shuagabannin ’yan kasuwar gwari na Sasa Ibadan, a ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwar Alhaji Usman Yako da shugaban ’yan Arewa mazauna garin na Sasa, Alhaji Isa Nalado Kabo suka kai wa masarautar Agege da ke Jihar Legas ziyarar ban girma ga Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Dogonkaɗai da yi masa ta’aziyyar mahaifiyarsa […]
A kwanakin baya ne shuagabannin ’yan kasuwar gwari na Sasa Ibadan, a ƙarƙashin jagorancin shugaban kasuwar Alhaji Usman Yako da shugaban ’yan Arewa mazauna garin na Sasa, Alhaji Isa Nalado Kabo suka kai wa masarautar Agege da ke Jihar Legas ziyarar ban girma ga Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammadu Dogonkaɗai da yi masa ta’aziyyar mahaifiyarsa wacce ta rasu a watan da ya gabata, inda suka nemi sabunta tsohon zumuncin ’yan kasuwar tare da masarautar ta Agege.
Shugaban ’yan Arewa ya shaida wa Aminiya cewa akwai daɗaɗɗiya kuma kyakkyawar alaƙa a tsakanin ’yan kasuwar Sasa Ibadan da masarautar Agege tun farkon zuwan ’yan Arewa Kurmi, waɗanda mafi akasarinsu ’yan kasuwa ne da ke harkar goro. Ya ce a lokacin ’yan kasuwar ta Sasa a nan masarautar Agege suke yada zango, kasencewarta masarauta ce da ’yan kasuwa suka kafa ta, wacce bayan lokaci ya sauya cinikin goro ya gushe, ’yan kasuwar suka sauya akalar kasuwancinsu zuwa kayan gwari da ake kawowa daga Arewa; sai wannan tsohon zumunci nasu ya yanke.
“Sai muka ga ya dace mu zo mu dawo da tsohon zumuncin nan na iyaye da kakkani,” inji shi.
A nasa ɓangaren, shugaban leburori a kasuwar ta Sasa Ibadan, Alhaji Rabe Ɗandume, ya shaida wa masarautar ta Agege cewa ’yan kasuwar sun daɗe suna fama da ƙalubale da dama, kana kasancewar masarautar ta Agege ce uwa ga ’yan Arewa a Kurmi, don haka za su yi amfani da wannan dama na sabunta zumuncinsu, su miƙa ƙoƙon bararsu domin a share masu hawaye a duk lokacin da buƙatan hakan ya taso.
Kakakin masarautar Agege, Alhaji Kabir Ali Dinar, Dallatun Agege, wanda ya yi jawabi da yawun masarautar a sa’ilin da sarkin Agege ya karɓi baƙuncin ’yan kasuwar, ya shaida cewa ’yan kasuwa ’yan Arewa mazauna Kurmi ne suka kafa masarautar sama da shekaru 160 da suka gabata, domin ci gaban harkokin zamantakewarsu da kasuwancinsu. Don haka masarautar ta yi murna da sabunta zumuncinsu da ’yan kasuwar na Sasa Ibadan suka yi kuma za su tabbata sun ba su duk wata gudunmawa da suke buƙata.
A ƙarshe mai martaba sarkin Hausawan Agege ya jagoranci addu’a ga ’yan kasuwar tare da nema masu albarka a harkokin kasuwancinsu. Haka kuma an yi addu’a ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da nema wa ƙasar nan dawwamammen zaman lafiya.