’Yan kasuwa sun kaurace wa kasuwar Shuwarin
Daruruwan ’yan kasuwa ne Suka kaurace wa kasuwar shuwarin a ranar Litinin da ta gabata saboda rashin ciniki da karancin kudade a wajan ’yan kasuwar. Wani dan kasuwa daga Karamar Hukumar Dutse mazaunin kauyan Rajo Malam Shehu Mahauci, ya bayyana haka ga wakilinmu na Jihar Jigawa a lokacin da yake ganawa da shi a kasuwar […]
Daruruwan ’yan kasuwa ne Suka kaurace wa kasuwar shuwarin a ranar Litinin da ta gabata saboda rashin ciniki da karancin kudade a wajan ’yan kasuwar.
Wani dan kasuwa daga Karamar Hukumar Dutse mazaunin kauyan Rajo Malam Shehu Mahauci, ya bayyana haka ga wakilinmu na Jihar Jigawa a lokacin da yake ganawa da shi a kasuwar Shuwarin Karamar Hukumar Kiyawa
Shehu ya ce “rashin zuwan ’yan kasuwar a ranar Litinin yana da nasaba da karancin kudi a wajen jama’a kuma da hauhawar farashin kaya saboda gabatowar Sallah da kuma maganar karin albashin ma’aikatan da ake ta zuzutawa.”
Shehu ya ce an tara shanu da raguna da awaki a kasuwar amma saboda talauci babu masaya, haka ake komawa gida da su kamar yadda aka kawo su kasuwar.
Ya kara da cewa saboda rashin zuwan ’yan kasuwar, sai a yi sukuwa da doki a kasuwar idan ka dauki layin masu sayar da kayan miya da ‘yan hula babu inda ake yin hada-hadar saye da sayarwa a kasuwar sai dai layin masu sayar da kayan abinci da wajen masu sayar da tuwo da abinci garau-garau.
Ya kara da cewa wannan alamu ne cewa an shiga wata irin rayuwa mara dadi a Najeriya.