‘Yan kasuwa sun koka da gwamnatin Filato
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Jihar Filato Mista danjuma Yerse ya ce gwamnatin jihar ba ta tallafa musu domin gudanar da harkokinsu ba. Ya bayyana haka ne yayin bikin rantsar da sababbin shugabannin kasuwannin da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a kwanakin baya.Ya ce yana so a shaida wa Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang cewa […]
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Jihar Filato Mista danjuma Yerse ya ce gwamnatin jihar ba ta tallafa musu domin gudanar da harkokinsu ba.
Ya bayyana haka ne yayin bikin rantsar da sababbin shugabannin kasuwannin da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa a kwanakin baya.
Ya ce yana so a shaida wa Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang cewa ’yan kasuwar sun jefa masa kuri’a a lokacin zabe, amma abin takaici ba su amfana da komai ba a wannan gwamnati ba.
Ya ce ’yan kasuwa suna da matukar mahimmanci a duniya. Don haka ya kamata gwamnati ta rika tallafa musu, domin a samu bunkasar tattalin arziki a kasar nan.
Ya bukaci ’yan kasuwar su fito zabi gudanar da zabe domin idan sun kai kukansu a rika share musu hawaye.
Ya ce “Mu ne muka fi kowa yawan kuri’a a kasar nan, don haka mu fito mu zabi wakilan da za su taimaka mana, sannan sababbin shugabannin kasuwannin da aka rantsar su rike amanar da aka damka masu tsakani da Allah, kuma su tashi tsaye su kama aiki a kasuwanninsu don a samu ci gaba.”