’Yan kasuwa sun koka da lalacewar tsohuwar hanyar Legas

Wasu ’yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a Kudu maso yammacin Najeriya sun koka bisa lalacewar hanyar nan ta Ilori zuwa Jaba a Jihar Neja, matsalar da suka ce ta yi kamari ne saboda ramuka da kwazazzai da ke kan hanyar, da ma ruwan saman da ake tafkawa wanda ya kara munana lamarin, domin […]

’Yan kasuwa sun koka da lalacewar tsohuwar hanyar Legas
’Yan kasuwa sun koka da lalacewar tsohuwar hanyar Legas

Wasu ’yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a Kudu maso yammacin Najeriya sun koka bisa lalacewar hanyar nan ta Ilori zuwa Jaba a Jihar Neja, matsalar da suka ce ta yi kamari ne saboda ramuka da kwazazzai da ke kan hanyar, da ma ruwan saman da ake tafkawa wanda ya kara munana lamarin, domin tun a farkon watan jiya, mota kanyi kwana 3 zuwa 4 a cikin cunkoson motoci a hanyar;  wanda hakan ke janyo mummunar asara ga ’yan kasuwa masu safarar kayayakin masarufi, mussanman kayan gwari da dabbobi. Sakamakon haka ne ire-iren kayayyakin farashinsu suka yi tashin gwaron zabi a kasuwannin kudancin kasar.
Alhaji Gambo Funtuwa mai sana’ar kayan hatsi ne a garin Shagamu. Ya shaida wa Aminiya cewa a duk ranar Laraba sai ya bi hanyar ya je Birnin Gwari, inda yake sayo hatsi ya kai Shagamu. Ya ce a da matsalarsu ta ’yan fashi ce a tskanin garin Funtuwa da Birnin Gwari amma a yanzu an sami saukin haka kwarai, a sakamakon sauyin gwamnati. Sai dai a yanzu babbar matsalar ita ce lalacewar hanyar, domin sai ka shafe kwana 4 idan ka  taso daga Birnin Gwari, tun daga Nasarawar Jaba har zuwa garin Olorun a Jihar Kwara, hanyar a lalace take, domin haka yake kira ga gwamnati da ta dubi halin da suke ciki ta kawo masu dauki.
Shi ko Alhaji Hamza Usman, wanda ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a garin Shagamu kuma Shugaban kungiyar Izala a Jihar Ogun, ya shaida wa Aminiya cewa hanyar na barazana ga harkokin kasuwancinsu, domin asarar da ake tabkawa ta yi muni. “Za ka ga mota ta dauko kayan gwari a tsaye cik, kayan sun zama ruwa sun tsiyaye. To ka ga mai kaya ya yi asara, ina maganar kudin direba ko na mai mota? Haka za ka ga dabobbi na ta kasawa, suna mutuwa sai in an yi da gaske za a yanka, a cire kayan cikin a zubar; a shanya su kafin a samu hanya ta bude. A wani wajen ma sai an sauke duk abin da babbar mota ta dauko kafin ta iya wucewa. Ai ka ga muna cikin halin ni ’yasu, mu talakawa da hanya muke neman abincinmu. Don haka muna bukatar dauki.” Inji shi.
Wani matashin direba mai suna Bashir Alhasan ya shaida wa Aminiya cewa tsohuwar hanyar Legas din ta fi kwanciyar hankali ga direbobin manyan motoci ta fuskar tsaro kuma ta fi sauri in an kwatanta ta da sabuwar  hanyar da ake bi ta Abuja, domin ta tsohuwar hanyar daga Legas zuwa Kano kilomita 1220, maimakon sabuwar hanyar da kilomita 1400 ne, wannan shi ne dalilin da ka ga direbobi sun nace wa wannan hanyar amma lalacewarta ta yi tsanani. A kwanakin baya ne wata motar tanki dauke da fetir ta fadi a hanyar ta kone, wata babbar mota da kan wata tirela da ke wajen, sai ka yi tafiyar kiloabamita 80 a hanyar ba tare da ka hau kwalta ba; sai muggan ramuka da kwazazzabai, domin wani ramin idan ka shiga da babbar mota sai ramin ya shanye tayar, baya ga ruwan da ke ciki da ramukan. Hakan yake haddasa faduwar manyan motoci dauke da kayayyakin masarufi, wanda ke sa ’yan kasuwa tafka mummunar asara.
Ba ’yan kasuwa da direbobi ne kawai ka cin kudarsu bisa tabarbarewar tsohuwar hanyar Legas ba, hatta ma shuwagabannin kungiyar dirabobin manyan motoci suna kokawa da lamarin. Shugaban kungiyar NURTW, Alhaji Muhammadu Bello Jibrin a Abbatuwa da ke Agege, ya shaida wa Aminiya cewa a halin da ake ciki, kazancewar lalacewar hanyar ta yi muni, domin tun gabatowar Sallah Babba har zuwa yanzu hanyar ta kara gurbacewa. Tafiyar da za ka yi daga Sakkwato zuwa Jaba ta awa 2, in ka iso yankin Odoba da Olorun sai ka yi kwana 7 a wajen, kana warin dabbobin da suke mutuwa a kan hanyar ma kawai ya isa ya dami mutum.  “Direbobi ne ke zuwa daji da kansu zu saro itatuwa su yi ciko domin motoci su sami wucewa, wasu su wuce wasu su kafe a wajen. Yawanci ’yan dako ne ke sauke kayan da manyan motoci ke daukowa su ketarar da su. Kiran da zan yi wa gwamnati shi ne, a duba halin da hanyar nan ke ciki, a kawo mana dauki, domin mu sami salama. Muna fatan sabbin ministocin da aka nada, wanda za a ba alhakin ayyuka da ya duba matsalar tsohuwar hanyar Legas, domin a gyara ta.” Inji shi.