’Yan kasuwa sun yi yaji a Isra’ila kan hare-haren Gaza
Babban titin harkokin kasuwanci da ke da galibin Palasdinawa a birnin Nazareth a kasar Isra’ila ya kasance a rufe a ranar Litinin, bayan da mazaunansa suka shiga yajin aikin gama-gari da zanga-zangar la’antar hare-haren mako biyu da Isra’ila ke kaiwa ga Zirin Gaza.Dubban shaguna da cibiyoyin kasuwanci a sassan kasar Isra’ila da gabar Kogin Jordan […]
Babban titin harkokin kasuwanci da ke da galibin Palasdinawa a birnin Nazareth a kasar Isra’ila ya kasance a rufe a ranar Litinin, bayan da mazaunansa suka shiga yajin aikin gama-gari da zanga-zangar la’antar hare-haren mako biyu da Isra’ila ke kaiwa ga Zirin Gaza.
Dubban shaguna da cibiyoyin kasuwanci a sassan kasar Isra’ila da gabar Kogin Jordan sun shiga yajin da aka shirya bayan kwana daya da zafafa hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza inda ta hallaka fiye da mutum100.
Dubban masu zanga-zanga sun rike kwalaye dauke da hotunan yaran da aka kashe lokacin hare-haren suna kiran sojojin kasar da “’yan ta’adda” ko “masu aikata laifin yaki.”
Masu zanga-zangar sun dan fafata da ’yan sanda bayan babbar zanga-zanga kuma an kama mutane da dama.
Zanga-zangar nuna kyamar yaki ta watsu a makon jiya a sassan kasar ciki hard a garin Haifa inda aka kama ko aka rika dukan ’ya’yan kungiyar Knesset, sai dai zanga-zangar ta ranar Littinin ta fi yawan jama’a da kuma tsari.
Wani mazaunin Nazareth Samir Haddad ya ce, “Matakin shi ne mai muhimmanci, a nuna goyon baya da bore ga miyagun laifuffuka. Muna bukatar mu nuna wa duniya cewa mu al’umma daya ne.”
Kiran yajin aikin kasar ya fusata Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Abigdor Lieberman wanda ya nemi magoya bayansa su kaurace wa ’yan kasuwar da suka shiga yajin.
“Ina kira ga kowa kada ya sayi komai daga shaguna da wuraren kasuwanci na al’ummar Larabawa da suk shiga yajin gama-gari yau,” ya rubuta a shafinsa na Facebook.
Kusan mutum 700 aka kama bayan zanga-zangar kamar yadda wata kungiyar kare hakkin jama’a ta ce, ciki hard a mutum 224 a yankin Gabashin kudus. Sai dai an saki galibinsu, amma an gabatar da dama a gaban kotu kan ttuhuamr jifa da duwatsu da ttare hanyoyi, kuma laifi na karshe ya dauki hukuncin daurin shekara 15.
Salah Mohsen na kungiyar kare hakkin jama’a ta Adalah ya ce “Wasu daga cikinsu an gurfanar da su ne, ko an bincike su saboda kawai sun yi amfani da shafin Facebook. Shugabannin wannan yunkuri da suka yi kira (ta intanet) don yin zanga-zanga, mun wasu daga cikinsu da aka bincika kuma aka tsare su.”