’Yan kasuwa za su yi karar Bankin Microfinance da AMATA

Wasu kananan ‘yan kasuwa a Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano za su yi karar kungiyar ’Yan kasuwa ta AMATA da kuma bankin bayar da rance ga kananan ‘yan kasuwa mai suna Grassroot Microfinance Bank bisa zarginsu da hadin baki wajen shirya musu almundahana cikin wani tsarin karbar bashi da suka tallata musu.‘Yan kasuwar sun […]

’Yan kasuwa za su yi karar Bankin Microfinance da AMATA
’Yan kasuwa za su yi karar Bankin Microfinance da AMATA

Wasu kananan ‘yan kasuwa a Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano za su yi karar kungiyar ’Yan kasuwa ta AMATA da kuma bankin bayar da rance ga kananan ‘yan kasuwa mai suna Grassroot Microfinance Bank bisa zarginsu da hadin baki wajen shirya musu almundahana cikin wani tsarin karbar bashi da suka tallata musu.
‘Yan kasuwar sun bayyana cewa tun farko kungiyar ta AMATA ce ta kawo musu wani fom na wannan bankin wanda aka rubuta balo-balo a jiki cewa tsarin bayar da rance ba tare da kudin ruwa ba,  haka kuma an nemi mutum ya bude asusu a bankin da kashi goma na kudin da yake son karbar bashi daga bankin.
“Hakan ya sa mutane suka gaggauta sayen fom  din inda suka cike shi tare da zuba kudinsu wato kashi 10 cikin dari. Daga baya ne sai kungiyar ta zo mana da wata zungureriyar takarda inda take bayanin cewa duk mutumin da ke son bashin sai ya biya wani kaso a matsayin ladan bankin, haka kuma ita ma AMATA sai an ba ta ladan ganin ido. Da muka ga haka sai muka je banki da niyyar mu kwashe kudinmu sai muka tarar labari ya sha bamban, domin bankin ya riga ya debi wani kaso na kudin daga ciki, akwai Naira dubu ta katin ATM da kuma wata dubu dayan ta kudin fam da wata Naira dubun ta ladan ajiya” Inji Abubakar Ibrahim daya daga cikin ’yan kasuwar.
‘Yan kasuwar sun kara da cewa wannan al’amari ya janyo tsayawar lamurran kasuwancinsu, domin mutane duk sun hade kudinsu sun zuba a wancan banki da niyyar neman bashi.  Hakan ya janyo tsayawar kasuwanci a wajen kananan ‘yan kasuwa, kasancewar duk mun dauki kudaden kasuwancinmu” Inji shi.
A karshe ‘yan kasuwar ta yi kira ga bankin da ya dawo musu da kudinsu, don a cewarsu babu kira babu abin da zai ci gawayi.
Aminiya ta tuntubi kungiyar AMATA inda Shugaban Kwamitin AMATA Mai kula da wannan bashin Musa Khalid Mohammad  ya bayyana cewa dama tun farko an yi abin ne da biyu, na farko a sama wa ’yan kasuwa jari, sannan kuma a gefe guda su ma banki suka samu kudin shiga
Ya ce: “Rashin fahimta aka samu a cikin al’amarin , domin su mutanen sun dauka cewa haka kawai za su sami kudi ba tare da ba wa banki ko kwabo ba.