’Yan kasuwan masallacin Baraka sun koka da matakin gwamnatin Kaduna

Wadansu ‘yan kasuwa a Jihar Kaduna sun koka game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tilasta musu tashi daga inda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a wurin da aka fi sani da masallacin Baraka da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja,A zantawarsa da Aminiya, Shugaban ‘yan kasuwan da ke gudanar da harkokinsu a […]

’Yan kasuwan masallacin Baraka sun koka da matakin gwamnatin Kaduna

Wadansu ‘yan kasuwa a Jihar Kaduna sun koka game da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tilasta musu tashi daga inda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a wurin da aka fi sani da masallacin Baraka da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja,
A zantawarsa da Aminiya, Shugaban ‘yan kasuwan da ke gudanar da harkokinsu a wannan wurin Adamu Abubakar, ya bayyana cewa, sun kwashe shekaru uku a wurin suna gudanar da kasuwancinsu, inda matafiya kan yada zango don cin abinci da dai sauran biyan bukatarsu ta yau da kullum . Ya kara da cewa a da kasuwar a Gonin Gora take ci, amma saboda rikicin bayan zaben shekarar 2011 ya sa suka yi kaura daga can,  sai suka tare a mazaunin kasuwar na yanzu wato gaban gidan gonan nan na Barakat da ke hanyar Abuja.
,Shugaban ‘yan kasuwan ya ce an umarces u ne da su tashi daga wurin cikin kwanaki bakwai ta hannun Mataimakin Shugaban
karamar Hukumar Chikun, kuma wa’adin ya cika ne a ranar Litinin da ta gabata.
Ko da wakilinmu ya ziyarci kasuwar kafin cikar wa’adin, ya tarar da wadansu daga cikin ‘yan kasuwan sun fara tashi daga wurin, ba tare da sanin inda za su koma ba. Kamar yadda suka ce gwamnati ta umarce su ne da su koma Sabon Gayan, amma ‘yan kasuwan sun ce can din wuri ne da akwai masu shi. Shugaban ‘yan kasuwan ya ce akalla mutane 2000 ke samun abincisu daga kasuwan don haka ya bukaci gwamnatin jihar da ta sake duba matakin da ta dauka da idon basira saboda rayuwarsu ta dogara da gurin.
Wani direba mai suna Ibrahim da Aminiya ta zanta da shi a kasuwar, ya bayyana damuwarsa  da umarnin tashin ‘yan kasuwan saboda a ce warsa, “fiye da motoci 1500 ne ke yada zango a wurin a kullum. Dalili da ya sa wurin kan zama ba masaka tsinke da fasinjoji a kodayaushe.” Inji shi
Direban ya kara da cewa, “idan aka ce su tashi, yanzu ina za mu yada zango ke nan? Muna zuwa nan ne saboda biyan bukatarmu da na fasinjojinmu.”
kokarin wakilinmu na ganawa da Babban Sakataren Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kaduna ya ci tura saboda an shaida masa cewa ya tafi Zariya. Haka kuma Kwamishinan Ma’aikatar Muhallin ma ba ya nan.  Amma wata majiya a Ma’aikatar wanda ta bukaci mu sakaya sunanta, ta shaida wa Aminiya cewa hukumar da ke kula kadarori ta Jihar Kaduna ce (KEPA) ta bai wa ‘yan kasuwan umarnin tashi daga wajen saboda zamansu a wajen ya saba wa doka.
“Muna sane da umarnin da aka ba su cewa su tashi saboda zamansu a wajen ya saba wa doka. Baya ga hakan kuma gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai duba yadda jama’a ke kafa shaguna a cikin gari da kuma zai yi aikin tabbatar da cewa suna bin doka da oda, nan gaba kadan ne dai kwamitin zai fara aikinsa.” Inji majiyar tamu.