‘Yan kasuwar Alaba Rago  sun nemi daukin shugabannin Arewa

’Yan kasuwar Alaba Rago da ke Legas sun nemi dauki daga shugabannin Arewa kan yunkurin da suka ce, ana yi na tashinsu daga kasuwar da suka gina fiye da shekara 40 da suka gabata. Alhaji Adamu Katagum Shugaban Gidauniyar Talaka kuma Wazirin Sarkin Kasuwar Alaba Rago, ya shaida wa Aminiya cewa, lura da yadda Shugabar […]

‘Yan kasuwar Alaba Rago  sun nemi daukin shugabannin Arewa

Shugabannin ‘Yan kasuwar Alaba Rago lokacin da suka halarci taron da Shugabar Qaramar hukumar Iba ta shirya musu

’Yan kasuwar Alaba Rago da ke Legas sun nemi dauki daga shugabannin Arewa kan yunkurin da suka ce, ana yi na tashinsu daga kasuwar da suka gina fiye da shekara 40 da suka gabata.

Alhaji Adamu Katagum Shugaban Gidauniyar Talaka kuma Wazirin Sarkin Kasuwar Alaba Rago, ya shaida wa Aminiya cewa, lura da yadda Shugabar Karamar Hukumar Iba, ke yunkurin rushe kasuwar ta kori jama’ar da ke kasuwanci a ciki ne ya sanya suka ga ya dace su sanar da shugabannin Arewa halin da ’yan kasuwar ta Alaba Rago suka tsinci kansu a ciki. “Domin Allah ne kadai Ya san adadin mutanen da ke cin abinci a kasuwar wadda ta kunshi kabilu daban-daban sai dai ’yan Arewa ne ke da kashi 90 cikin 100 na masu kasuwanci a Kasuwar Alaba Rago, don haka muke kira ga shugabanninmu na Arewa su kawo mana dauki domin idan aka samu matsala al’ummarsu za ta fi shafa,” inji shi.

Ya ce, ya yi zama da wadansu daga cikin shugabannin ’yan Arewa da suka hada da Sanata Kabiru Gaya, sannan sun yi zama da uban Jam’iyyar APC na Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, “Mun ziyarci Sanata Kabiru Gaya mun shaida masa halin da muke ciki ya yi alkawarin share mana hawaye, dama can shi mutum ne mai tausayin talakawa da damuwa da koke-kokensu. Ya ba mu tabbacin taimakonmu, mun gode masa. Za mu yi amfani da wannan dama mu mika kukanmu ga sauran shugabannin Arewa. Shi ma Asiwaju Bola Tinubu da muka je masa da maganar ya saurare mu ya kuma ba mu tabbacin a kowane lokaci yana tare da jama’a ne, don haka mu kwantar da hankalinmu, babu wanda zai kore mu daga kasuwar,” inji shi.

Ya ce, Shugaban Kasa Janar Murtala Muhammad ne ya ba su filin da suka gina kasuwar a 1975 inda aka bai wa Hausawa Kasuwar Alaba Rago, aka bai wa kabilar Ibo Kasuwar Alaba ta Duniya sai sai kasuwar da ke tsakanin Alaba Rago da Kasuwar Alaba ta Duniya wacce ake kira Tanzaniya wacce aka bai wa Yarbawa amma su sai suka sayar da tasu. “Mu masu biyayya ne, fatarmu a ba mu damar yin gyarar kasuwar da kanmu, domin muna tsoron kada a yi mana bi-ta- da-kulli,” inji shi.

A baya Shugabar Karamar Hukumar Iba, Uwargida  Ramat Rachel Oseni inda Alaba Rago take, ta kira taron shugabannin  kasuwar da wasu daga cikin shugabannin al’ummar yankin inda ta bayyana masu manufarta game da kasuwar. Ta ce gyara za ta yi, domin inganta kudin shiga da karamar hukumar ke samu daga kasuwar da kuma kyautata rayuwar ’yan kasuwar.

Amma ’yan kasuwar sun nuna tsoron kada a karshe a raba su da shagunansu idan karamar hukumar ta jagoranci gyara kasuwar