‘Yan Kasuwar Bakin Asibitin Murtala sun koka kan kudin rumfuna
Masu kasa kayayyakin sayarwa a kan titin Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano fadar Jihar Kano sun koka game da abin da suka kira ‘halin da Karamar Hukumar Birni ke shirin jefa su a ciki’ inda suka nemi taimakon Gwamnatin Jihar Kano don kawo musu sauki. A kwanakin baya ne Karamar Hukumar Birni […]
Masu kasa kayayyakin sayarwa a kan titin Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano fadar Jihar Kano sun koka game da abin da suka kira ‘halin da Karamar Hukumar Birni ke shirin jefa su a ciki’ inda suka nemi taimakon Gwamnatin Jihar Kano don kawo musu sauki.
A kwanakin baya ne Karamar Hukumar Birni da Kewaye ta yanka wa ’yan kasuwar biyan Naira dubu goma-goma kowannensu a matsayin kudin wurin da suke zama don gudanar da kasuwancinsu idan ba haka ba kuma sai dai su bar wurin.
’Yan kasuwar da ke sayar da kayayyaki daban-daban sun ce su masu karamin jari ne don haka ba za su iya biyan wannan kudi da karamar hukumar ta gindaya musu ba.
Daya daga cikin ’yan kasuwar, Malam Ibrahim Ali ya ce “Mu kananan ’yan kasuwa ne, ba wani jari gare mu ba. Idan an duba yawancinmu dukkan kayayyakin da muke sayarwar ba su wuce Naira dubu biyu ba kowannenmu, to wanda ke cikin wannan hali yaya ma za a yi ya iya biyan wannan kudi?”
Wani mai sayar da kanwa a kasuwar mai suna Ibrahim Bashir ya bayyana matakin na karamar hukumar a matsayin wani abu na rashin tausaya wa ’yan kasuwar lura da halin da ake ciki a kasa na rashin kudi a hannun mutane wanda yake janyo rashin ciniki ga ’yan kasuwar.
‘Yan kasuwar sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullah Umar Ganduje ya kai musu dauki ta hanyar hana Karamar Hukumar Birni aiwatar da abin da ta yi niyya.
Sai dai Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Birni Alhaji Danbello Aminu ya ce karamar hukumar ta yanke wannan hukunci ne lura da cewa ’yan kasuwar sun dade suna gudanar da kasuwancinsu kara-zube ba tare da wani tsari mai kyau ba. “Tunda dadewa suke gudanar da kasuwanci a wannan waje babu wata takarda daga gwamnati ta shaidar zama a wurin , don haka muka ga dacewar su karbi takarda ta shaidar zama a wurin. Idan suka biya wannan kudi za a ba su takardar shaidar mallakar wurin kasuwanci na wuncin-gadi.
Da aka yi masa nuni kan batun masu karamin jari a cikin ’yan kasuwar sai ya ce “To duk wanda yake ganin yana da karamin jari ba zai iya biya ba, sai ya bar wurin domin akwai masu so sai su karba. Shi kansa teburin da suke amfani da shi ya kai Naira dubu biyar ashe idan za ka iya ajiye irin wannan teburi yaya mutum zai ce wai jarin dubu biyu gare shi? Wannan batun biyan kudi abu ne da babu gugu babu ja da baya a kansa.”
Alhaji Danbello ya yi kira ga ’yan kasuwar su daina nuna karaya a duk lokacin da gwamnati ta zo musu da wani abu da zai amfane su. “Idan ka duba wannan abu zai amfani ’yan kasuwar sannan a waje daya gwamnati za ta amfana domin za ta kara samun hanyar kudin shiga. Ina ganin kamata ya yi ’yan kasuwar su yi murna da wannan abu da aka kawo musu lura da cewa abu ne da zai tsarkake harkar kasuwancinsu. Domin a yanzu za su samu izinin zama a wurin sabanin baya da za a iya korarsu a kowane lokaci,” inji shi.