’Yan kasuwar Bodija sun koka kan rashin cika alkawarin gwamnati

Shugaban fataken wake na kasa, Alhaji Bala Kano ya ce har yanzu gwamnatin Jihar Oyo ba ta cika alkawarin bayar da tallafi ga ’yan kasuwar Bodija Ibadan da suka yi hasarar kaya da kadarori na fiye da Naira miliyan 12 a dalilin boren da ’yan kasuwa Yarbawa suka yi a cikin watan Agusta ba. ’Yan […]

’Yan kasuwar Bodija sun koka kan rashin cika alkawarin gwamnati

Shugaban Fatake, Alhaji Bala KanoShugaban fataken wake na kasa, Alhaji Bala Kano ya ce har yanzu gwamnatin Jihar Oyo ba ta cika alkawarin bayar da tallafi ga ’yan kasuwar Bodija Ibadan da suka yi hasarar kaya da kadarori na fiye da Naira miliyan 12 a dalilin boren da ’yan kasuwa Yarbawa suka yi a cikin watan Agusta ba. ’Yan kasuwa Yarbawan dai sun yi boren ne wai domin huce hushi da daukar fansa a kan Hausawan, saboda mutuwar wasu Yarbawa a hannun ’yan boko haram a Jihar Borno.
Boren na watan Agusta, ya haifar da daukar matakin rufe kasuwar na tsawon kwanaki bakwai. Bayan shawo kan al’amarin ne, Gwamna Abiola Ajimobi ya yi bikin bude kasuwar tare da yi wa iyalan mamatan da kuma ’yan kasuwar da suka yi hasara, alkawarin bayar da tallafi. A farkon watan jiya ne gwamnan ya bayar da tallafin Naira miliyan 28 ga iyalan ’yan kasuwar da suka rasa rayukansu a Jihar Borno.
Cikin hirarsu da wakilinmu a Ibadan, Shugaba Alhaji Bala Kano, ya ce, “Kamar yadda Gwamna Abiola Ajimobi, ya yi mana alkawari tare da ba mu muhimmiyar shawarar mu kafa kungiyoyin gama kai domin tafiya da murya daya wajen samun irin tallafin da aka saba bayarwa ga irin wadannan kungiyoyi domin bunkasa harkokin kasuwanci a jihar, mun karba. Da farko dai, a kungiyance, tuni mun kammala tantance irin barnar da aka yi mana ta kayan abinci da kadarori, kuma mun mika rubutattun bayanan komai da ya shafi mutanenmu baki daya ta hannun lauyanmu domin aikewa ga shugabannin kasuwa da kuma shugaban karamar Hukumar Ibadan ta Arewa, amma har yanzu babu wani bayani da ya iso gare mu. Mun shirya bin sawu domin tunatarwa ga shugabannin kasuwa da shugaban karamar hukuma, wadanda gwamnan ya ce mu mika musu bayanan namu.”
Ya ce tuni sun yi nisa wajen wayar da kan kungiyoyi daban-daban irin muhimmancin gamayyar kungiyoyi kuma sun fara ganin alamomin nasara a cikin shirin. “Muna farin ciki da kuma jinjina wa Gwamna Abiola Ajimobi, musamman saboda kokarin janyo mu a kusa da gwamnati da yake yi, saboda ya lura da harkokin kasuwancinmu na kayan abinci suna taimaka wa wajen bunkasar tattalin arzikin jihar. Saboda haka, muke daukar matakan ganin dukkan ’ya’yan kungiyoyin ’yan kasuwa Hausawa da ke zaune a jihar ta Oyo, sun bayar da cikakken hadin kansu da goyon bayan shirye-shiryen da gwamnatin jihar ke yi domin ci gaban al’umma baki daya.” Inji shi.
A karshe ya bayyana muhimmancin matsayinsu na kasancewa masu girmama doka da oda da kyautata zamantakewarsu da jama’ar gari, lamarin da shi ne zai kai su ga mike kafaf domin gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da tsangwama ba.