’Yan kasuwar dabbobi a Kurosriba sun koka da matsin lamba
Har yanzu ’yan kasuwa da ke fataucin dabbobi daga Arewacin kasar nan zuwa kudancinta na ci gaba da kokawa da matsalolin da suke fuskanta da kuma tasku a hannun masu karbar kudin jangali da kuma jami’an da ake jibgewa kan manyan hanyoyin kasar nan suna sintiri. Mafi yawan ’yan kasuwar da suka kawo dabbobinsu Kurmi […]
Har yanzu ’yan kasuwa da ke fataucin dabbobi daga Arewacin kasar nan zuwa kudancinta na ci gaba da kokawa da matsalolin da suke fuskanta da kuma tasku a hannun masu karbar kudin jangali da kuma jami’an da ake jibgewa kan manyan hanyoyin kasar nan suna sintiri.
Mafi yawan ’yan kasuwar da suka kawo dabbobinsu Kurmi domin sayarwa a makon jiya sun bayyana cewa kasuwa ta ci ta watse amma an samu kwashe, wanda hakan suka danganta shi da lamari ne na kasuwanci wanda kowane dan kasuwa ya saba ganin haka a harkar.
Alhaji Ishaka Muhammad Hadeja, wani dan kasuwa da ya kawo raguna sayarwa a kasuwar, ya bukaci gwamnati ta sake waiwayar baya domin sanar da rushe masu karbar kudin haraji da jangali da ta sanar kwanan baya. “Yanzu sun dawo suna ci gaba da yi wa mutane wulakanci da kuma karbar kudin yadda suka ga dama. Haka za su sara wa mutum ko ya biya ko kuma su hana mota tafiya ba tare da yin tunani ko la’akari da irin asarar da za su jawo wa mai dabbobin ba,” inji shi.
Shi kuwa Mukhtar Ahmad Abubakar da ke kasuwar dabbobi ta Nasarawa Bacoco, a hirarsa da Aminiya ya bayyana cewa ban da matsalar mota da za ta daukar masu kaya, wasu karin matsalolin da suke fuskanta idan sun dauko masu sun hada da tsadar kudin mota da kuma matsi a hannun jami’an tsaro da sauransu.
Hka kuma ya kara kawo wani hanzari da yake nuna irin yadda jami’an tsaro masu sintiri da masu karbar kudin jangalli suke yi wa kowace mota idan ta dauko kaya daga Arewaci “A rabano wato jangali da kuma haraji, muna kashe kudi masu yawa daga motaci masu taya 12 zuwa masu taya 10. Abin da ya kama fakas, ya kama J5, kusan kowacce kudinta a kayyade yake. Ka ga kamar watannin baya, mota taya 12 a Makurdi sukan karbi har Naira dubu 30 a kan kowacce tirela,” inji shi.