’Yan kasuwar dabbobi ta Abuja sun koka kan rashin banki

Masu sayar da dabbobi a kasuwar dabbobi ta Abuja da ke Deidei sun koka a kan rashin bankuna a cikin kasuwarsu duk da fulotai biyu da aka ware a cikin tsarin taswirar kasuwar don a gina bankuna.  Shugaban ’yan kasuwar, Sarkin Zangon Deidei Alhaji Muhammadu Sada Kusada ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa […]

’Yan kasuwar dabbobi ta Abuja sun koka kan rashin banki
’Yan kasuwar dabbobi ta Abuja sun koka kan rashin banki

Masu sayar da dabbobi a kasuwar dabbobi ta Abuja da ke Deidei sun koka a kan rashin bankuna a cikin kasuwarsu duk da fulotai biyu da aka ware a cikin tsarin taswirar kasuwar don a gina bankuna. 

Shugaban ’yan kasuwar, Sarkin Zangon Deidei Alhaji Muhammadu Sada Kusada ne ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da Aminiya a ranar Litinin.
Alhaji Sada ya ce kasuwar wadda aka fara aikin gina ta a lokacin tsohon Ministan Abuja Jerimiah Usene, sannan aka kaddamar da ita a lokacin Ministan Abuja Malam Nasir Ahmad el-Rufa’i, ya ce duk da hada–hadarta tare da kasancewa mahada ga ’yan kasuwar dabbobi na Kudu da na Arewa, ’yan kasuwarta na zuwa kasuwar gini ta Abuja ne wanda ke nesa da wajen, ko kuma garin Zuba, ko Kubwa don yin huldar banki a yanzu haka.
Ya ce hakan na jawo musu babbar matsala kasancewar wasu abokan huldarsu da bukatar banki ta kama na gwammace dakatar da hulda a maimakon fuskantar hadarin zuwa bankunan. Shugaban ya ce idan an kafa banki a kasuwar zai taimaka musu har ma da sauran al’umma a garin Deidei, wanda ke matsayin dandalin manyan motoci a Abuja.
Sauran matsalolinsu a cewar shugaban, sun hada da rashin karasa tituna a cikin kasuwar, sannan ba a turo jami’an tsaro a karamin ofishin ’yan sanda da ke mashigarta ba,