’Yan kasuwar kabeji a Jos sun zabi sababbin shugabanni

’Yan kabeji da ke farar gada a garin Jos a Jihar Filato sun zabi sababbin shugabannin kasuwar a makon jiya. Shugabannin da aka zaba sun hada da Malam Tanimu Isah Aliyu a matsayin Shugaba da Usman Adam Haruna Mataimakin Shugaba na I da Muhammad Sani Ciroma Mataimakin Shugaba na II da Shehu Adam Sakatare da […]

’Yan kasuwar kabeji a Jos sun zabi sababbin shugabanni
’Yan kasuwar kabeji a Jos sun zabi sababbin shugabanni

’Yan kabeji da ke farar gada a garin Jos a Jihar Filato sun zabi sababbin shugabannin kasuwar a makon jiya.

Shugabannin da aka zaba sun hada da Malam Tanimu Isah Aliyu a matsayin Shugaba da Usman Adam Haruna Mataimakin Shugaba na I da Muhammad Sani Ciroma Mataimakin Shugaba na II da Shehu Adam Sakatare da Sani Lawal dan Mai unguwa Mataimakin Sakatare.
Sauran shugabannin su ne: Annafi Haruna Sakataren Tsare-tsare da Adam Usman Jume Jami’in Hulda da Jama’a da Auwal Ahmad Sakataren Kudi da Isah Bello Mai Binciken Kudi da kuma Ibrahim Buraima mai bayar da shawara.
Sabon Shugaban Malam Tanimu Isah Aliyu ya ce babu shakka wannan zabe da aka yi musu shi ne zakaran gwajin dafi a tarihin kafa wannan kasuwa, musamman ganin irin yadda kusan dukkan ’yan kasuwar suka jefa kuri’unsu.
Ya ce za su kare ’yancin ’yan kasuwar tare da inganta harkokin kasuwanci a wannan kasuwa.
Ya bukaci ’yan kasuwar da sauran jama’ar da suke zuwa kasuwar su kara ba su goyan baya da hadin kai, don su cim ma wadannan kudurori da suka sanya a gaba.