’Yan kasuwar Kano sun buƙaci kawo ƙarshen zanga-zangar yunwa

‘Yan kasuwar sun ce tattaunawa ita kaɗai mafita game da matsalolin da ake fuskanta a ƙasar.

’Yan kasuwar Kano sun buƙaci kawo ƙarshen zanga-zangar yunwa

Wasu ’yan kasuwa a Jihar Kano, sun yi kira ga matasa da su dakatar da zanga-zangar yunwa tare da rungumar tattaunawa a matsayin hanyar magance ƙorafe-ƙorafensu.

Sun yi wannan kiran ne bayan jawabin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Cikin wata da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya yi da wasu mazauna jihar, sun yarda cewa tattaunawa ita ce hanya ɗaya tilo da za a warware matsalolin da suke addabar jama’r ƙasar nan.

Sun jaddada cewa shugaban ƙasar ya amince da ƙorafe-ƙorafen masu zanga-zangar kuma a shirye yake domin a yi tattaunawa.

Wani ɗan kasuwa a jihar mai suna Taiye Hassan, ya yaba wa jawabin shugaban ƙasar, kuma ya bukaci masu zanga-zangar da su bayar da ƙofa domin tattaunawa.

Ya ce duk da matsalolin yunwa da rashin tsaro da ake fuskanta, ya dace masu zanga-zangar su karɓi tayin shugaba Tinubu don yin masalaha.

Shi ma wani ɗan kasuwa, Bala Muhammad, ya bayyana shugaban ƙasar a matsayin mai tausayi kuma mai kare dimokuraɗiyya.

Ya kuma yi kira ga masu zanga-zangar da su karɓi tayin shugaban don tattaunawa.

Ya gargaɗi masu zanga-zangar da su guji bari wasu mutane suna amfani da su wajen cimma mummunan muradansu.

Malama A’isha Ibrahim da ɗan jarida Nura Imam, sun kuma goyi bayan kiran shugaban ƙasa na yin zama domin tattaunawa.

Sun yi kira ga masu zanga-zangar da su kwantar da hankalinsu tare da gabatar da buƙatunsu ta hanyar da ta dace, domin samun bakin zaren gyaran matsalolin.

Sun jaddada mjhimmancin kishin ƙasa da haɗin kai a tsakanin matasa.