’Yan Kasuwar Kofar Ruwa sun koka kan gini a bakin shagunansu
’Yan kasuwar Kofar Ruwa a Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano sun koka kan karin wasu gine-gine da aka yi musu a bakin shagunansu inda suka yi zargin Karamar Hukumar Dala ce da alhakin wannan badakala. ’Yan kauswar sun ce a safiyar ranar Litinin ne suka wayi gari da ganin sababbin gine-gine a bakin shagunansu […]
’Yan kasuwar Kofar Ruwa a Karamar Hukumar Dala a Jihar Kano sun koka kan karin wasu gine-gine da aka yi musu a bakin shagunansu inda suka yi zargin Karamar Hukumar Dala ce da alhakin wannan badakala.
’Yan kauswar sun ce a safiyar ranar Litinin ne suka wayi gari da ganin sababbin gine-gine a bakin shagunansu wanda suke kyautata zaton cikin tsakiyar daren ranar Lahadi aka gudanar da shi.
Wadansu daga cikin ’yan kasuwar musamman wadanda ke kasa kaya a bakin titi sun yi zargin an sace musu kayayyakinsu a yayin da aka gudanar da wancan gini.
Malam Muhammad Sabi’u wani da aka yi wa gini a bakin rumfarsa ya ce a yanzu haka ko rumfarsa bai bude ba saboda babu wurin da zai ajye kayan kasuwancinsa kamar yadda ya saba. “A gaskiya wannan gini cuta ce a gare mu domin ginin da aka yi ya rufe mana shagunanmu babu wanda yake ganinmu. Sannan dan wurin da muke ajiye kayanmu a kofar shagonmu shi ma mun rasa saboda wannan gini da aka yi a tsakanin shagona ko kafa biyar bai kai ba. Bayan kuma yau ko wata biyu ba a yi ba karamar hukuma ta sayar mana da gaban shagunanmu a kan Naira miliyan daya kuma sai ga shi an zo an sake sayar wa wadans,” inji shi.
Malam Abdullahi Sulaiman wanda ke yin sana’ar facin taya ya ce an kwashe masa taya guda 40 sakamakon wannan gini da aka yi.
“To ni dai a wannan wuri nake sana’ar facin taya, to sai na zo na samu an kwashe min kayana an kuma dora gini a wurin da nake sana’ar. Yanzu ina neman a taimaka min a dawo min da kayayyakina domin da shi nake neman abincina da na iyalina,” inji shi.
’Yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati ta gaggauta rushe ginin saboda a wurin ne suke neman abinci. “Duk da cewa mun ga gwamnati ta zo ta shafa jan fenti na umarnin a dakatar da ginin, to hakan bai isa ba. Muna so gwamnati ta yi kokarin rushe ginin cikin gaggawa domin a wanann wuri da aka dora ginin nan muke karkasa kayayyakinmu. Mun shafe kimanin shekara 21 muna gudanar da harkokinmu a wannan wuri. Kimanin mutum dubu daya ne ke cin abinci a wannan wuri. Kuma muna biyan haraji yadda ya kamata. Idan har aka kore mu daga wannan wuri shi ke nan mun rasa abin yi,” inji shi.
Alhaji Isyaku shi ne Shugaban Babbar Kungiyar ’Yan Kasuwar Kofar Ruwa ya bayyana rashin jin dadinsa game da wannan abu da ya faru inda ya ce, “Baya ga toshe shagunan ’yan kasuwarmu da wadannan sababbin gine-gine da aka yi da kuma hana wadansu kananan ’yan kasuwa yin kasuwancinsu a wannan wuri, ginin da aka yi idan aka duba an yi shi ne a kan kuskure domin a kan kwata aka yi shi sannan akwai wayayoyin wutar lantarki da suka bi ta kan ginin wanda duk mai hankali ya san cewa za a iya samun hadari a wurin.”
Shugaban ’yan kasuwar ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano a karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi gagagwar warware wannan matsala don guje wa aukuwar tashin hanakali.
Sai dai duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Karamar Hukumar Dala abin ya ci tura, inda aka shaida mata cewa Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Ali ’Yan Tandu ne kadai ke da alhakin yin magana kan wanann batu shi kuma a yanzu Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar ta dakatar da shi a kan wani batu na daban.