’Yan kasuwar Kuros Riba na kyamar sabuwar Naira 100
Wasu daga cikin al’umma da kananan ’yan kasuwa a Jihar Kuros Riba suna kyamar sabuwar takardar kudi ta Naira 100 wadda Gwamnatin Tarayya ta kaddamar 12 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata domin murnar cika shekara dari da hadewar bangarorin kasar nan wuri guda da ake kira a yau Najeriya.Binciken da Aminiya ta gudanar […]

Wasu daga cikin al’umma da kananan ’yan kasuwa a Jihar Kuros Riba suna kyamar sabuwar takardar kudi ta Naira 100 wadda Gwamnatin Tarayya ta kaddamar 12 ga watan Nuwambar shekarar da ta gabata domin murnar cika shekara dari da hadewar bangarorin kasar nan wuri guda da ake kira a yau Najeriya.
Binciken da Aminiya ta gudanar a birnin Kalaba fadar Gwamnatin Jihar Kuros Riba, tsakanin ’yan kasuwa da suke gudanar da harkokin kasuwanci ya nuna wasu daga cikinsu suna kyamar sabuwar takardar kudin.
Tun farko ma sai da kungiyoyin kwadagon kasar nan suka yi tir da wancan hobbasa da wannan gwamnati ta yi game da kudin, amma gwamnati ta jajirce wa alummar kasa cewa ba da wata manufa aka bullo da takardar kudin ba duk da haka takardar ta Naira 100 na shan kyara da kyama saboda a cewar jama’a samfurinta ya abambanta da wadda jama’a suka sabada ita.
Madam Eka-ette Kufre wata ’yar kasuwa ce kuma ta shaida wa wakilinmu cewa: “Allah ya kiyaye banaso, a bani wadda na sani yaya zanyi in yarda wanna takardar kudin Najeriya ce bayan an sauya mata fasali,” injita. Wasu kuma da sukayi nasu korafin sun nuna cewa wannan takardar kudin suna tsoro za a iya samun jabunta don haka ba ta da wani kwarjini.
Alhaji Sadik Ibrahim ya shaidawa Aminiya cewa: “ Ni ba ta da wata tasiri a gareni a wurin kasuwata domin ni idan na karba ina karba sai dai matsalar idan ni nabayar da ita wajen canji idan an sayi kayana mutanen ba su yarda da ita, kuma su ba su yi mini bayanin dalilan da ya sanya suke kyamarta ba,”inji shi.
Amma da wakilinmu ya nemi jin ta bakin ofishin Babban Bankin Najeriya reshen Jihar Kuros Riba game da batun, hakarsa ba ta cimma ruwa ba saboda babu wani wanda ya yarda ya ce wani abu game da lamarin.