’Yan kasuwar Lafiya sun yi zanga-zangar adawa da canja musu matsuguni

A ranar Litinin da ta gabata ne dubban ’yan kasuwar Babban Kasuwar Lafiya a Jihar Nasarawa suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yunkurin gwamnatin na sauya musu matsuguni zuwa sabuwar kasuwar birnin, inda suka yi zargin an dora musu kudi mai yawa wajen karbar hayar shagunan da ke cikinta. Da yake zantawa da manema […]

’Yan kasuwar Lafiya sun yi zanga-zangar adawa da canja musu matsuguni
’Yan kasuwar Lafiya sun yi zanga-zangar adawa da canja musu matsuguni

A ranar Litinin da ta gabata ne dubban ’yan kasuwar Babban Kasuwar Lafiya a Jihar Nasarawa suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yunkurin gwamnatin na sauya musu matsuguni zuwa sabuwar kasuwar birnin, inda suka yi zargin an dora musu kudi mai yawa wajen karbar hayar shagunan da ke cikinta.
Da yake zantawa da manema labarai a Lafiya, shugaban masu zanga-zangar Usman Shitu ya ce ’yan kasuwar sun dauki wannan mataki ne don nuna bakin cikinsu da rashin amicewa da yunkurin gwamnatin jihar na canja musu kasuwar daga inda take zuwa sabuwar kasuwar, wadda a cewarsa maimakon gwamnati ta ba su hayar shagunan sabuwar kasuwar su rika biyan ta, sai ta ba masu hannu da shuni da ’yan siyasa inda su kuma suke ba su hayarsu da tsada.
Ya ce “Kudin hayar shaguna a sabuwar kasuwar da yanzu take hannun ’yan siyasa da masu hannu da shuni ya fi karfinmu kasancewa muna fuskantar rashin ciniki.”
Shugaban masu zanga-zangar ya ce gwamnati ta ba masu hannu da shufi kowane shago a farashin Naira dubu 50, kowace shekara amma su kuma suna ba ’yan kasuwa kan Naira dubu 100, shi ya sa suke zanga-zangar.  
Ya ce har ila yau gwamnati ta ba su mako biyu ne kacal su koma sabuwar kasuwar wanda bai dace ba.
Daraktan Labarai na Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, Alhaji Ahmed Tukur ya kare manufar gwamnati inda ya ce gwamnati ba ta da wata mummunar manufa kan mayar da kasuwar sabon matsugunin. Ya ce gwamnati ta dauki matakin ne don gina hanyoyi a babbar kasuwar saboda a rage cinkoso kasancewa a yanzu kasuwar tana samun karuwar jama’a, gas hi tana tsakiyar gari.
Ya musanta zargin da ’yan kasuwar suka yi cewa ba a sanar da su a kan lokaci ba inda ya ce gwamnati ta jima da sanar da su inda ta ba su sama da wata uku kafin wannan lokaci. Ya ce a kwanakin baya ’yan kasuwar sun ba gwamnati wasu sharudda da za su inganta canjin kasuwar, inda a cewarsa nan take gwamnati ta amince da su ta kuma cika musu alkawari. Ya shawarci ’yan kasuwar su rungumi matakin na gwamnati don ta yi ne don amfaninsu da al’ummar jihar.
A kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta gina sabuwar kasuwa ta zamani inda tunda aka kammala ta take umurtar ’yan kasuwar su koma cikinta.