‘Yan kasuwar lemo sun kalubalanci zaben shugabancin kasuwar
A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar ’Yan kasuwar Kayan marmari ta ‘Yan lemo da ke Jihar Kano ta gudanar da zaben shugabannin kungiyar wadanda za su ja ragamar kungiyar a shekarar da aka sake zaben Shugaban kasuwar Alhaji Muhammadu na Alhaji Alto a matsayin shugaban kungiyar. Sai dai zaben ya bar baya […]
A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyar ’Yan kasuwar Kayan marmari ta ‘Yan lemo da ke Jihar Kano ta gudanar da zaben shugabannin kungiyar wadanda za su ja ragamar kungiyar a shekarar da aka sake zaben Shugaban kasuwar Alhaji Muhammadu na Alhaji Alto a matsayin shugaban kungiyar.
Sai dai zaben ya bar baya da kura sakamakon kauracewa zaben da wasu ‘ya’yan kungiyar suka yi inda suka zargi shugabannin kungiyar da gudanar da zabe ba bisa ka’ida ba. Alhaji Sadik Adullahi Yarima shi ne tsohon Sakataren tsare-tsare na kungiyar ’yan kasuwar ya shaida wa Aminiya cewa zaben da kungiyar ta gudanar haramtacce ne duba da yadda kungiyar ta yi watsi da umarnin Gwamnatin Jihar Kano a kan kada a gudanar da zaben. “Wannan zabe muna kallonsa a matsyain haramtacce, domin gwamnati ta bayar da umarni kada a gudanar da zaben, amma shugabannin kungiyar su 18 suka yi fatali da wanann umarni na gwamnati, inda suka je suka gudanar da zaben a boye a wani wuri a garin Kwanar dangora su kadai, ba tare da sanin sauran ’ya’yan kungiyar ba, har suka rantsar da kansu,” inji shi.
Ya bayyana cewa su suna biyayya ga gwamnati, za kuma su ci gaba da zama a matsayinsu na shugabannin kungiya, har zuwa ranar 6 ga watan Maris lokacin wa’adin shugabancinsu zai cika.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben, Alhaji Idris Abubakar Gwangwan ya musanta zarge-zargen, inda ya ce sun gudanar da zaben ne bisa umarnin kotu.
A cewarsa: “duk da cewa gwamnati ta hannun Kwamishinan kasuwanci ta hana gudnar da zaben hakan ya sa muka je kotu, inda kotu ta ba mu takarda (court order) akan hakan, ya sa muka gudanar da zabenmu. Mun yi imani da mu da gwamnati duk a karkashin doka muke.”
Haka kuma shugaban ya bayyana cewa sun gudanar da zabensu a bayyane wanda aka yi shi lami lafiya ba tare da wata hayaniya ba.
“Mun yi zabe lafiya a gaban kowa, hakan ya sa wadanda suka fadi a zaben suka goyi bayan sakamakon zaben, inda suka sallama tare da alkawarin mara wa sababbin shugabannin baya wajen gudanar da al’amuran kasuwar gaba daya,” inji shi.
Alhaji Idris ya bayyana cewa mutanen da ke wadannan surutai ba su da wata hujja a kan zarge-zargen nasu illa adawa kawai.
“Mu a wurinmu wadanda ke wadannan surutai ba ‘ya’yan kungiyarmu ba ne, kasancewar ba su yi rajista da kungiyar ba. Muna kallonsu ne a matsayin ‘yan adawa kawai,” inji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga sauran ’yan kasuwa da su zauna lafiya tare da mayar da hankali kan al’amuran kasuwancinsu don ci gaban Jihar Kano.