‘Yan Kasuwar Rimi sun koka game da ginin rumfunansu

’Yan Kasuwar Rimi a Kano sun koka game da tilasta su da Karamar Hukumar Birni ta yi cewa sai sun dora dakin maimakon rufin kwano a sababbin rumfunan da suke ginawa a cikin kasuwar. Aminiya ta gano cewa Karamar Hukumar Birni da Kewaye ce ta cire rumfunan kwano da ke kasuwar tare da sayar wa […]

‘Yan Kasuwar Rimi sun koka game da ginin rumfunansu

Malam Salisu Ya’u Yola Shugaban Qungiyar Yan Kasuwar Rimi aJihar Kano

’Yan Kasuwar Rimi a Kano sun koka game da tilasta su da Karamar Hukumar Birni ta yi cewa sai sun dora dakin maimakon rufin kwano a sababbin rumfunan da suke ginawa a cikin kasuwar.

Aminiya ta gano cewa Karamar Hukumar Birni da Kewaye ce ta cire rumfunan kwano da ke kasuwar tare da sayar wa ’yan kasuwar wurin inda kuma ta umarci kowane mai rumfa ya gina kayansa da kansa.

’Yan kasuwar sun ce idan har damina ta fadi a wannan lokaci to ba su san yadda za su yi da kayayyakinsu ba kasancewar a yanzu suna ajiyewa a fili ba tare da  da wurin ajiye kaya ba.

Har ila yau ’yan kasuwar sun yi kokafin rage musu girman rumfunansu da karamar hukumar ta yi inda hakan ya janyo wadansu da dama daga cikinsu ba su san wurin da za su kai kayansu su ajiye ba..

Wani sashe daga ginin sababbin shagunan da yan kasuwar ke korafi a kai

Malam Zakari Shehu ya bayyana wa Aminiya cewa tunda suka fara gina rumfunan nasu wanda karamar hukumar ce ta kawo ma’aikatan da ke gudanar da aikin, aikin yake tafiyar hawainiya inda har suka nemi karamar hukumar ta sahale musu su ci gaba da gudanar da aiki da kansu.

“Kin ga a da rumfata tana daukar kayayyaki da yawa amma a yanzu ba za ta dauki wadannan kayayyakin ba. Haka da a ce an ba mu dama da tuni mun yi aikinmu da kanmu saboda su masu yi mana aikin ma’aikatan karamar hukuma ne kuma ba su yin sauri wajen aiki,” inji ta.

Malam Salisu Ya’u Yola shi ne Shugaban Kasuwar Rimi, ya bayyana cewa suna sane da aikin ginin rumfunan da Karamar Hukumar Birni ta sanya ’yan kasuwar su yi, amma ba su san yadda aka shirya gudanar da aikin ba.

“Tunda farko kwamitin da Karamar Hukumar Birni ta kafa ya zo ya samu kungiya inda ya bayyana mana manufarsu na son canja tsarin kasuwar ta hanyar cire rumfunan kwano tare da mayar da su ginannun shaguna. Babu shakka mun yi murna da lamarin domin ci gaba ne a gare mu. Sai dai lokacin da za a fara aikin babu wanda ya sanar da mu za a fara aikin ko ga yadda za a gudanar da aikin har sai daga baya da abin ya rikice sannan muka sani,” inji shi.

Shugaban Kungiyar Kasuwar ya bayyana cewa duk da cewa ’ya’yan kungiyar ba su sanar da su lokacin da suka biya kudinsu ba, amma a matsayinsu na kungiya za su nemi karamar hukuma don tattaunawa a kan korafe-korafen ’yan kasuwar.

“ Duk da cewa lokacin da ’yan kasuwar suka ba karamar hukuma kudinsu ba su sanar da mu ba. Amma dai a matsayinmu na iyayen kungiya za mu san abin da za mu yi don ganin an shawo kan lamarin,” inji shi.

Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Karamar Hukumar Birni abin ya ci tura kasancewar Shugaban Karamar Hukumar ba ya nan, haka kuma bai amsa kira da sakon tes da wakiliyar Aminiya ta aika masa ta wayarsa ba.