‘Yan Kasuwar Sabon Gari sun fara watangaririya sanadiyar sake wa kasuwar fasali
A ranar Juma’a da ta gabata ce wa’adin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba ’yan Kasuwar Sabon Garin Zariya, na su tashi ya cika sakamakon kudirin gwamnatin na rusa kasuwar da sake mata fasali. Kasuwar Sabon Garin Zariya tana daya daga cikin manyan kasuwanni da ke Jihar Kaduna, kuma tana daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da […]
A ranar Juma’a da ta gabata ce wa’adin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba ’yan Kasuwar Sabon Garin Zariya, na su tashi ya cika sakamakon kudirin gwamnatin na rusa kasuwar da sake mata fasali.
Kasuwar Sabon Garin Zariya tana daya daga cikin manyan kasuwanni da ke Jihar Kaduna, kuma tana daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da aka dade ana saye da sayarwa a cikinsu.
Aminiya ta ga yadda wadansu da aka fara rushe rumfunansu suke ta watangaririyar neman wajen da za su tsuguna domin ci gaba da kasuwancinsu.
Wani dan kasuwar da ke kasuwar, Alhaji Muhammad Sani Dan Yusha’u wanda aka fi sani da Kwata-Miliyan ya bayyana sake fasalin Babbar Kasuwar Sabon Gari da abin alfahari ga ’yan kasuwar.
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a harabar kasuwar, inda ya ce, abu daya da suke rokon a yi musu shi ne, a waiwayi masu gidaje da ke kasuwar domin a ba su damar mallakar rumfuna kamar yadda aka yi wa sauran ’yan kasuwa.
Alhaji Sani Kwata-Miliyan ya ce, kasancewar Gwamna Nasiru El-Rufa’i mai fada da cikawa ne, ya kamata ya ji rokonsu domin a yi musu adalci.
A cewarsa, su masu bin doka ne kuma suna mutunta shugabanni don haka ne a maimakon tayar da hankali sai suka amince da yin addu’a ga gwamnati domin ta samar wa jama’arta ci gaba mai amfani.
Wani dan kasuwar Malam Abdullahi Sani, wanda wakilinmu ya zanta da shi a sabon matsugunin da suke kokarin gyarawa domin ci gaba da kasuwancinsu ya ce, “A da mun shiga rudani kasancewar ba mu samu inda za mu koma da harkokin saye da sayarwarmu ba, amma zuwa yanzu gwamnati ta sama mana wurin zama, muna fata Allah Ya sa haka ya zame mana alheri.”
Shi ma da yake bayani game da aikin kasuwar Shugaban ’Yan Kasuwar Sabon Gari, Alhaji Ibrahim Mai Gwal ya ce, an fara kashin farko na aikin inda ’yan kasuwar da aikin ya shafa suka koma tsohon filin wasa na Sabon Gari don ci gaba da kasuwancinsu kafin a kammala aikin su dawo.
Alhaji Ibrahim Mai Gwal ya ce an tsara yadda za a mallaki rumfa bayan an kammala aikin, wanda tsarin ke da matakai biyar kuma duk mai bukatar rumfa, to zai yanki fom da zai nuna irin rumfar da yake bukata sannan zai ajiye kashe 10 na kudin rumfar da yake bukata.
Ya ce za a yi wa kowa adalci in an kammala aikin wajen mallakar rumfa amma sun bai wa masu rumfuna a kasuwar muhimmanci inda suka hana wadansu daga wajenta shigowa don mallakar rumfuna.