’Yan Kasuwar Sabon Gari sun nemi agajin Majalisar Kano
Gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da ke Sabon Garin Kano sun nemi Majalisar Dokokin ta jihar ta yi duba na tsanaki a kan wata doka da ke gabanta a kan kasuwar wacce suka ce za ta kassara harkokin kasuwancinsu. Da yake jawabi ga Shugaban Majalisar a kan batun, Shugaban Kungiyar ’yan […]
Gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da ke Sabon Garin Kano sun nemi Majalisar Dokokin ta jihar ta yi duba na tsanaki a kan wata doka da ke gabanta a kan kasuwar wacce suka ce za ta kassara harkokin kasuwancinsu.
Da yake jawabi ga Shugaban Majalisar a kan batun, Shugaban Kungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Alin Bagadaza ya ce hakika dokar za ta kawo koma baya a harkokin ’yan kasuwa da dama.
- Marainiya gurguwa mai rarrafen kilomita 1 kullum zuwa makaranta
- Budurwa ta banka wa masoyinta wuta don ya ki aurenta
- Buhari ya kori Shugaban Hukumar Samar da Ayyuka
Ya kuma bayyana rashin gamsuwarsa a kan jagorancin shugaban kasuwar, Alhaji Uba Zubairu Yakasai inda ya ce zuwansa a matsayin shugaba a kasuwar ya haifar da lalacewar harkokin kasuwancinsu.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Abdul’azeez Garba Gafasa ya ce Majalisar za ta tuntubi dukkanin wadanda dokar ta shafa domin tabbatar da ganin an yi wa kowane bangare adalci.
Ya bayyana cewa majalisar za ta yi duk wani yunkuri da zai samar da zaman lafiya da bunkasa harkokin ’yan kasuwar.
Shugaban Majlisar wanda ya nuna jin dadi bisa nuna halin da’a da bin matakin da ya dace wajen shigar da kokensu, ya kuma ba ’yan kasuwar tabbacin cewa Majalisar za ta yi kokarin ganin dokar ta zama masalaha ga ’yan kasuwar kafin su amince da ita.