‘Yan Kasuwar Sheikh Gumi muna tare da El-Rufa’i – Daudawa

Qungiyar ’Yan Kasuwar Sheikh Abubakar Gumi da ke Kaduna sun musanta rade-radin da ke zagayawa  cewa wai wata qungiyar masu kasuwanci a kasuwar ta tsame kanta daga cikinsu, cewa ba ta cikin wadanda suka saya wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i fom din tsayawa takara. A kwanakin baya ne aka riqa yada wata sanarwa […]

‘Yan Kasuwar Sheikh Gumi muna tare da El-Rufa’i – Daudawa
‘Yan Kasuwar Sheikh Gumi muna tare da El-Rufa’i – Daudawa

Qungiyar ’Yan Kasuwar Sheikh Abubakar Gumi da ke Kaduna sun musanta rade-radin da ke zagayawa  cewa wai wata qungiyar masu kasuwanci a kasuwar ta tsame kanta daga cikinsu, cewa ba ta cikin wadanda suka saya wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i fom din tsayawa takara.

A kwanakin baya ne aka riqa yada wata sanarwa daga wata qungiyar ’yan kasuwar ta Sheikh Gumi a qarqashin shugabancin Alhaji Falalu Musa Maidoya da Alhaji Gafai Boska da Mista Thomas Yakubu wadanda suka fitar da takardar cewa ba su tare da wadanda suka saya wa Gwamna El-Rufa’i fom din tazarce.

Qungiyar ’Yan Kasuwar ta Sheikh Gumi ta bayyana cewa ba ta san wadancan mutane ba sannan qungiyar ma ba su san da ita ba. Takardar da Shugaban Qungiyar Ibrahim Daudawa ya sanya wa hannu ta ce su ba su san wadancan mutane ba.

“Ba mu san wadannan mutane ba, kuma muna roqonsu da su bayyana fuskokinsu kowa ya gansu. Mutane ne da ba su son zaman lafiya, suna neman su ta da fitina ne a inda babu ita,” inji Daudawa.

Ibrahim Daudawa ya qara da cewa suna so su sanar da mutane cewa ba sa tare da wadancan mutane sannan ba su tare da su. “Bayan haka su sani cewa mun sanar wa jami’an tsaro domin su gudanar da bincike a kai domin a gano ko su wane ne suka yi shigar burtu don bata mana suna,” in ji shi.