’Yan kasuwar Terminus sun koka kan yadda jami’an tsaro ke addabarsu

’Yan kasuwa da ke Kasuwar Terminus a garin Jos sun koka kan yadda jami’an tsaron da Gwamnatin Jihar Filato ta girka a kasuwar ke hantararsu da kuma cin zarafinsu. ’Yan kasuwar sun bayyana cewa jami’an tsaro suna kwacewa hade da lalata musu kayayyakinsu wadanda suka hada da takalma da kayayyakin sawa da jakankuna da sarkoki […]

’Yan kasuwar Terminus sun koka kan yadda jami’an tsaro ke addabarsu

’Yan kasuwa da ke Kasuwar Terminus a garin Jos sun koka kan yadda jami’an tsaron da Gwamnatin Jihar Filato ta girka a kasuwar ke hantararsu da kuma cin zarafinsu.

’Yan kasuwar sun bayyana cewa jami’an tsaro suna kwacewa hade da lalata musu kayayyakinsu wadanda suka hada da takalma da kayayyakin sawa da jakankuna da sarkoki da sauransu.

’Ya kasuwar sun yi koken ne ta bakin Shugaban kungiyar Masu Sayar da Takalma, na Jihar Filato, Alhaji Nasiru Yahaya a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a garin Jos.

Alhaji Yahaya ya ce abin bakin ciki ne irin yadda gwamnati take yi wa sha’anin ’yan kasuwa rikon sakainar kashi a jihar.

Ya ce, “Mu kananan ’yan kasuwa ne, inda kafin zaben 2015 Gwamna Lalong ya yi alkawarin idan ya ci mulki zai sake gina mana kasuwarmu, har yanzu da nake magana da kai ba a kai ga yin hakan ba, inda yau tsawon shekara daya kuma jami’an tsaro suna cin zarafinmu.”

“Sun lalata mana kayayyakinmu, inda wani lokaci mukan ji rauni a lokacin da muke tsere wa kamun jami’an tsaro. Don haka idan gwamnati ba za ta iya tallafa wa kasuwancinmu ba, to bai kamata ta lalata mana abin da ke hannunmu ba,” inji shi.

’Yan kasuwar sun ce har yanzu suna nuna goyon bayansu ga Gwamna Simon Bako Lalong duk da irin kalubalen da suke fuskanta, don haka suka bukaci ya sanya jami’an tsaro su bar su don su ci gaba da kasuwancinsu kafin ya kai ga gina musu kasuwarsu.

A lokacin da Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun ’yan sandar Jihar Filato, wato Mataimakin Sufurtanda, Tyopeb Terna sai ya karya zargin da ’yan kasuwar suke yi na cewa jami’ansu na cin zarafinsu.

Ya ce, “Tun lokacin da tagwayen bama-bamai suka fashe a kasuwar, inda suka janyo asarar rayuka da dukiya, sai gwamnati ta yanke hukunci rage cunkoso a garin, hakan ya sanya aka tashe su daga wurin da suke kasuwanci kasancewar wurin kan hanya ne, wadannan masu korafi, ya kamata su sani cewa masu shaguna a cikin kasuwar ma suna korafin sun tare musu kwastomominsu.”

Ya ce wurin da suke gudanar da kasuwanci ya saba ka’ida, kuma “Ina so in sanar da kai cewa jami’an tsaron da suke wurin ba su ci zarafin kowa ba, kuma suna gudanar da aikinsu bisa doka da tsari.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna