‘Yan Kasuwar Wayoyi na kofar Mata sun nemi tallafin gwamnati
Masu sayar da wayoyin hannu da ke Kasuwar Al-Ihsan a kofar Mata, Kano sun nemi gwamantin jihar ta tallafa musu da jari, kasancewar a yanzu haka da yawa daga cikin ’yan kasuwar va su da jari a hannunsu. Nazifi Garva Dattako shi ne Mataimakin Shugavan kungiyar ’yan kasuwar, ya vayyana cewa “A kasuwar nan kullum […]
Masu sayar da wayoyin hannu da ke Kasuwar Al-Ihsan a kofar Mata, Kano sun nemi gwamantin jihar ta tallafa musu da jari, kasancewar a yanzu haka da yawa daga cikin ’yan kasuwar va su da jari a hannunsu.
Nazifi Garva Dattako shi ne Mataimakin Shugavan kungiyar ’yan kasuwar, ya vayyana cewa “A kasuwar nan kullum mutane karyewa suke yi savoda karancin jari a hannunsu. A gefe daya kuma ga rashin ciniki sakamakon tavarvarewar tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan. Idan ya kasnace mutum yana da dan jari a hannunsa komai kankantarsa in ya zo kasuwa ya dan juya, to zai samu dan avin da zai koma gida ya ciyar da iyalinsa, amma a yanayin da mutum va ya da jarin juyawa kin ga va shi da wata mafita.”
Ya kara da cewa “A duk mako mukan dan hada kudade a tsakanin junanmu don taimakon kanmu kamar idan mutum va ya da lafiya ko mutuwa da sauransu. Amma va mu yi karfin da za mu taimaka wa junanmu da jari va. Muna kallo ’yan kasuwarmu suna samun karayar arziki amma vavu avin da za mu iya yi musu savoda rashin nauyin asusunmu.”
Mataimakin Shugava ya nemi gwamnatin Jihar Kano ta tallafa musu kamar yadda take tallafa wa sauran vangarorin ’yan kasuwa a jihar kamar masu shayi da masu sufuri da A Daidaita Sahu da sauransu. “Muna rokon idan gwamnatin za ta vayar da tallafin ta samar da tsarin da za a tavvatar tallafin ya isa gare mu. Domin a lokuta da dama gwamnati kan vayar da tallafi amma sai ya makale a wani wuri. Haka kuma a lokuta da dama za ki ga an zo an kawo mana fam, amma tun daga lokacin da muka cike va mu sake jin tashin zance va. Don Allah gwamnati ta tallafa mana ko da da vashi ne da za mu rika viya a hankali,” inji Dattako.
Ya ce kungiyarsu na kokarin daukar matakan da suka kamata wajen ganin ’yan kasuwarsu va su yi mu’amala da vatagari va, musamman masu kawo kayan sata cikin kasuwar.