‘Yan Katakon kasuwar Na’ibawa na bukatar ofishin kwana-kwana’
Masu hada-hadar kasuwancin katako a Kasuwar Katako ta Na’ibawa cikin Jihar Kano ta nemi gwamnati da ta samar musu da ofishin kwana-kwana a kusa da kasuwarsu, duba da irin yanayin kayan da suke sayarwa wanda gaba dayansa makamashi ne. Wannan kira ya fito ne daga Sakataren kungiyar Masu Sayar Da katako na kaswar Alhaji Auwalu […]
Masu hada-hadar kasuwancin katako a Kasuwar Katako ta Na’ibawa cikin Jihar Kano ta nemi gwamnati da ta samar musu da ofishin kwana-kwana a kusa da kasuwarsu, duba da irin yanayin kayan da suke sayarwa wanda gaba dayansa makamashi ne.
Wannan kira ya fito ne daga Sakataren kungiyar Masu Sayar Da katako na kaswar Alhaji Auwalu Abdussalam Adamu a yayin da yake tatauanwa da Aminiya.
Alhaji Auwalu ya bayyyana cewa samar da ofishin hukumar kashe gobara a kusa da su yana da muhimamnci duba da yawan kasuwannin da kuma tashoshin mota da ke unguwar wadanda al’ummar jihar da dama ke neman abinci a wurin.
“Tun daga kofar Nassarawa har zuwa Gadar Tamburawa babu ofishin kashe gobara. idan muka duba wadannan wuri namu ya kunshi kasuwanni masu yawa, baya ga kasuwarsu ta ’yan katako akwai ta ‘Yan lemo da kuma ta Kwanar Dawaki da kuma tashoshin mota wuraren da ke da muhimmanci kwarai da gaske a jihar, duba da dimbin jama’ar da ke neman abinci a wuraren don haka samar musu da ofishin kwana-kwana yana da muhimamnci.”
Sakataren kungiyar ya kara da cewa “duk da dai kungiya a nata bangren tana daukar mataki na hana abkuwar tashin gobara a kasuwar ta hanyar tabbatarwa an kashe duk wata wuta da aka kunna don jin dumi ko kuma wacce masu shayi ke kunnawa. Da kanmu shugabanni muke yawo mu tabbatar da an kashe wutar. A lokuta da dama mukan yi wa masu shayin nan bita akan kokarin kiyaye afkuwar gobara.”
Har ila yau kungiyar ta bayyana cewa tana neman gwamnati da ta bude musu wata hanya don shigowa cikin kasuwa, tare da samar musu da fitilu a cikin kasuwa. “akwai wata hanyar shigowa cikin kasuwa wacce ke kusa da ofishin yan sanda na Na’ibawa wacce aka rufe ta lokacin da ake fama da rigingimun ’yan tayar da kayar baya wanda a wancan lokacin mun goyi bayan hakan da aka yi kwarai da gaske. Amma a yanzu tunda zaman lafiya ya samu a jihar muke rokon gwamanti ta bude mana hanyar, don manyan motocin dake kawo mana kaya tare da fita da su su sami hanyar shiga kasuwa ba tare da matsala ba.”
Sakatare Alhaji Auwalu ya kuma yi kira ga gwamnati da ta tallafa way an aksuwarsu da jari ko da kuwa bashi ne. “Mu dai ba mu taba samun tallafin gwmanati ba, duk kuwa da cewar muan da rajista da gwamnatin tarayya da kuma ta jiha. Don haka muke roko a tallafa wa ’yan kasuwarmu da jari koda kuwa bashi ne. idan gwamnai za ta a mu wnaann tallai ya kamata ta gudanar da shi ta hanayar kungiya domin a samu saukin wajen sha’anin biyan bashin da sauna abubuwa da za su iya tasowa.”
Ya bayyana cewa shugabancin kungiya yana kula da harkar tsaron kasuwa da kuma gyaran kasuwa, “duk da cewa ba ma da nisa da ofihin ’yan sanda kungiya ta dauki ma’aikata kimanin 12 da ke kula da shige da fice na kasuwa. Misali babu mai shigowa kasuwa sai karfe bakwai na safe ta yi a haka kuma da zarar karfe bakwai na dare yay i kowa zai fita daga kasuwa, koda kuwa kaya aka kawo ba za a sauke ko a dauka ba sai da iznin shugabancin kungiya.
Kuma mun ba wa kowane dan kasuwa dama ya dauki maigadi nasa saboda kula da dukiyarsa musamamn cikin dare, duba da yanayin kayanmu ko ba don kula da kayan ba, ko don saboda yiwuwar tashin gobar, idan aka samu irin haka wanda ba a fata, musamman a cikin dare idan mutum yana da mai kula masa da kaya shi ke nan abubuwa za su zo cikin sauki.
Ya bayyaa cewa a tsawon shekaru 32 da suka dauka suna gudanar da kasuwanci a wannan kasuwar ta bunkasa ta fuskar kasuwanci da kuma yawan jama’a.
“Idan mun yin la’akari da yadda aka fara kasuwancin katako a wannan kasuwa a baya, za mu iya bugar kirji mu ce wannaan kasuwa a yanzu ta bunkasa. Baya ga mu masu sayar da katako a kasuwar nan akwai masu yanka da gugar katako da akwai leburori da direbobi wadanda yawanmu yakai dubu biyu,” inji shi.
Har ila yau ya bayyana cewa suna gudanar da harkar kasuwancinsu na katako ne ta fuskoki biyu wanda ya hada da masu gini da kuma masu yin kayan daki. Haka kuma ya bayyana cewa suna samun katako ne daga jihohin kudu da suka hada da Jihar Ekiti da Oyo da Osun da Neja da Kaduna da Zamfara da sauransu.