‘Yan kauye sun kashe mai garkuwa da mutane a Katsina
Wasu ‘yan kauyen Unguwar Bello a karamar hukumar Kafur a jihar Katsina sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne. Wanda ake zargin da aka kashe sun shiga kauyen ne tare da tawagarsa da nufin yin garkuwa da wasu. Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce ‘yan bindigar sun […]
Wasu ‘yan kauyen Unguwar Bello a karamar hukumar Kafur a jihar Katsina sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne.
Wanda ake zargin da aka kashe sun shiga kauyen ne tare da tawagarsa da nufin yin garkuwa da wasu.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah, ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne da misalin karfe 2 tsakar dare, inda suka kai hari kauyen tare da yin harbe-harbe amma ‘yan kauyen suka dakile harin.