’Yan kunar bakin wake sun halaka mutum 10 a Maiduguri

’Yan sanda biyar da fararen hula uku sun rasa rayukansu lokaci da ’yan kunar bakin wake suka kara motarsu dauke da bam a jikin motar ’yan sanda a wajen birnin Maiduguri da ke Jihar Borno a ranar Talatar da ta gabata.Wannan shi ne karo na biyu bayan harin da aka kai babban barikin soja a […]

’Yan kunar bakin wake sun halaka mutum 10 a Maiduguri
’Yan kunar bakin wake sun halaka mutum 10 a Maiduguri

’Yan sanda biyar da fararen hula uku sun rasa rayukansu lokaci da ’yan kunar bakin wake suka kara motarsu dauke da bam a jikin motar ’yan sanda a wajen birnin Maiduguri da ke Jihar Borno a ranar Talatar da ta gabata.
Wannan shi ne karo na biyu bayan harin da aka kai babban barikin soja a ranar Juma’ar da ta gabata inda wadanda ake tsare da su da dama suka gudu wasu kuma sojoji da ’yan banga suka halaka su daga baya.
Tashin bam din yaauku ne a kusa da Dalori da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Bama a kusa da Jami’ar Maiduguri.
 Rahotanni daga babban asibitin birnin sun ce an kai gawarwakin mutum biyar.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce mutum 11 ne suka rasu ciki har da ’yan sanda biyar.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa masu kunar bakin waken sun kara wa motar ’yan sanda inda aka ji karar fashewar bam din a tsawon kilomitoci.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Borno Gideon Jibrin ya tabbatar wa manema labarai rasuwar ’yan sanda biyar da fararen hula uku. Kuma wakilinmu wanda ya isa wurin ya iske an dauke gawarwakin, sai dai ya iske baswajan da aka kai harin da ita dauke da konannun gawarwakin maharan a ciki.  
A wani labarin kuma Dakarun Najeriya sun ce sun gano jibgin makamai da aka binne a wani cocin da aka kona, a karamar Hukumar Kalabalge da ke Jihar Borno.
Wata sanarwar da rundunar sojan Najeriya ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Manjo Janar Chris Olukolade ta ce, cikin makaman har da bindiga mai harbo jiragen sama da bindiga mai sarrafa kanta da dubban alburusai.
Sanarwar ta ce wani dan ta’adda da ya yi ikirarin cewa dan kasar Kamaru ne, shi ya kai su maboyar makaman da aka adana, domin kai hare-hare a garuruwan da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru.
Rundunar ta kara da cewa an kwashe dukkan makaman, kuma sojoji na ci gaba da sintiri, domin tabbatar da tsaro a yankin da kewayensa.