’Yan kunar bakin wake sun matsa da kai hare-hare a Maiduguri

’Yan kunar bakin wake sun matsa da kai hare-hare a kasuwanni da tashoshin mota a garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno, inda a cikin mako daya suka hallaka kusan mutum 100, bayan da sojojin kawance suka takura musu wajen kwato garuruwan da suke karkashin Boko Haram. A karshen makon jiya ne maharan da ake zargin ’yan […]

’Yan kunar bakin wake sun matsa da kai hare-hare a Maiduguri
’Yan kunar bakin wake sun matsa da kai hare-hare a Maiduguri

’Yan kunar bakin wake sun matsa da kai hare-hare a kasuwanni da tashoshin mota a garin Maiduguri hedkwatar Jihar Borno, inda a cikin mako daya suka hallaka kusan mutum 100, bayan da sojojin kawance suka takura musu wajen kwato garuruwan da suke karkashin Boko Haram.

A karshen makon jiya ne maharan da ake zargin ’yan Boko Haram ne, suka kai hare-hare a Kasuwar Kifi ta Tashar Baga da Babbar Kasuwar Maiduguri (Monday Market) da tashar mota ta Borno Edpress mallakar gwamnatin jihar.
Hukumomi sun ce mutum 58 ne suka rasu a hare-haren uku, to amma daya daga cikin matasan sa-kai na Sibiliyan JTF, mai suna Bukar Mala, ya shaida wa wakilinmu cewa hare-haren uku sun ci rayukan fiye da mutum 100.
Harin bam na ranara Talata ya ci rayukan mutum 20, bayan da aka yi zargin cewa wata ’yar kunar bakin wake ta tayar da bam a Shataletalen El-Kanemi kusa da kasuwar Monday Market da karfe 4:00 na yamma.
Wani mai suna Ali Sada da ke sayar da lemu a baro, ya ce, “Na ga yarinyar da ba ta wuce shekara 15 ba, ta shiga wani shago da ake sayar da kayan abinci, a kusa da shatale-talen mai hada-hadar jama’a. Ta ce wa mai shagon ya ba ta taliyar Indomi, kafin a dauko mata sai tana ta danna waya cikin tsoro da firgici. Da na ga haka sai na tashi daga wurin, kuma tashina ke da wuya sai muka ji karar bam a shagon, ko da muka je wurin sai muka ga yarinyar ce a mace rike da wayar da wasu na’urori, shi ya sa na tabbatar cewa ita ce ta dauko bam din.”
A ’yan kwanakin nan sojojin kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da Najeriya, sun tashin haikan wajen yakar Boko Haram, inda suka ce sun kwato garuruwa fiye da 30 ciki har da Gamboru da Monguno da Baga da Dikwa.