’Yan kungiyar asiri 120 sun tuba a Legas
Wasu ’yan ƙungiyar asiri da suka addabi mutanen yankin Imota da Ikorodu a Jihar Legas sun tuba sun aje makamansu a gaban Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas da babban basaraken lardin Imota, wanda ya jagoranci bikin karɓar tubarsu a fadarsa, bayan ya kai su wurin bautarsu na gargajiya, inda aka yi masu wankan tuba. Babban […]
Wasu ’yan ƙungiyar asiri da suka addabi mutanen yankin Imota da Ikorodu a Jihar Legas sun tuba sun aje makamansu a gaban Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas da babban basaraken lardin Imota, wanda ya jagoranci bikin karɓar tubarsu a fadarsa, bayan ya kai su wurin bautarsu na gargajiya, inda aka yi masu wankan tuba.
Babban Basaraken Oba Ronodu, ya shaida wa Aminiya cewa na baya da su ma za su kauce wa ɗabi’ar shiga ƙungiyar asiri. “Da safen nan ne muka kai su wajen bautarmu ta gargajiya, inda muka yi masu wankan tuba, aka tsaftace su. Za mu tabbatar mun ci gaba da wannan shiri,” inji shi.
Kwamishinan ’yan sandan, Edgal Imohimi ya bayyana shirin tubar da ’yan ƙungiyoyin asirin a matsayin muhimmin abu da zai kawo ƙarshen fargabar da al’ummar yankin ke fama da ita. Ya ce: “Ba adadin makaman da suka ajje ko yawan ’yan ƙungiayar asirin da suka tuba ne abu mafi mahimmanci ba, a’a, ganin yadda suka aje makamansu da karan kansu, suka tuba shi ne abin lura. Don haka ina kira ga sauran shuwagabannin al’umma da su yi koyi da babban basarake na wannan yankin, wajen sauya mutanensu daga gurɓataciyyar hanya zuwa turbar tsira,” inji shi
’Yan ƙungiyoyin asirin na Ayyeh da Ehyyeh, waɗanda a baya ba su ga maciji da juna sun yi ta rungumar junansu, suna rera waƙen zaman lafiya. Shugaban ’yan ƙungiyar asiri na Ayyeh na lardin Imota, Joseph Fasasi ya shaida wa Aminiya cewa: “Ganin yadda miyagun ayyukanmu na ƙungiyoyin asiri ke neman tagayyara yankin namu, har ta kai ga jama’a da dama na yin ƙaura suna barin gidajensu, ta yadda ƙasa ko gidan haya ba su daraja a wannan yankin, hakan ne ya sanya muka yi karatun ta-natsu, muka ga ya dace mu aje makamanmu don ci gaban yankinmu,” inji shi.
A baya dai yankin Imota da Ikorudu da kewaye ya yi fama da matsalar ƙungiyoyin tsageru masu fasa bututun man futir, baya ga ƙungiyoyin asiri da masu yin garkuwa da mutane. Malam Muhammad Hafiz a garin Imota aka haife shi. Ya shaida wa Aminiya cewa a baya a kowane lokaci hankalin jama’ar yankin a tashe yake. “Kimanin mako biyu ke nan ’yan ƙungiyar asirin suka kashe wani mahauci. Da ma shi ma ɗan ƙungiyar ne, bayan da suka kashe shi sai suka cire kansa suka zo tsakiyar gari suka aje. A haka ya yi kwana biyu a wajen, jama’a na wucewa suna gani wannan ne ya tayar da hankalin mutanen garin, har aka kai ga ɓullo da shirin tubar da ’yan ƙungiyar asirin,” inji shi.
Mafi akasari ‘yan ƙungiyoyin asirin kan yi kashe-kashen a tsakaninsu ne ba tare da sun taɓa wanda ba ya cikinsu ba, sai dai irin miyagun ayyukan nasu kan tada hankalin jama’a