’Yan kungiyar asiri sun kashe dalibi a Ibadan

Wadansu ’ya’yan kungiyar asiri a Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke Ibadan sun kashe wani dalibin makarantar mai suna Ahmed Olalekan da aka fi sani da Maku. dalibin yana daya daga cikin kungiyar dalibai masu yaki da miyagun ayyukan da ’yan kungiyar asirin suke yi. Wani dalibin makarantar mai suna Bello Isa ya shaida wa […]

’Yan kungiyar asiri sun kashe dalibi a Ibadan
’Yan kungiyar asiri sun kashe dalibi a Ibadan

Wadansu ’ya’yan kungiyar asiri a Kwalejin Kimiyya da kere-kere da ke Ibadan sun kashe wani dalibin makarantar mai suna Ahmed Olalekan da aka fi sani da Maku. dalibin yana daya daga cikin kungiyar dalibai masu yaki da miyagun ayyukan da ’yan kungiyar asirin suke yi.

Wani dalibin makarantar mai suna Bello Isa ya shaida wa Aminiya cewa, “Sun kashe dalibin ne a cikin daren Litinin da ta gabata a dakinsa da ke kauyen Apete, kusa da makarantar. Sun fara harbinsa da bindiga a wuyansa daga baya suka rika sararsa da gatari da adda domin su tabbatar da ya mutu. Wadannan dalibai masu tsafe-tsafe a cikin makarantar sun sha aikewa da sakon gargadi ga marigayi Maku cewa ya daina kyamar ayyukan da suke yi, idan ya ki ji to za su gama da shi.” 

Bello Isa wanda ya ce aukuwar wannan lamari ya haifar da zanga-zangar da daliban makarantar suka yi washegari ranar Litinin.

Kakakin kungiyar dalibai masu adawa da kungiyar asiri, Mista Adeyemi Ridwan yana daga cikin wadanda suka yi wa marigayin gaisuwar karshe kafin rasuwarsa. Ya ce, “Makonni 2 da suka wuce matsafan daliban sun rika yin barazanar kawo mana hari, inda muka sanar da mahukuntan makarantar a kan haka.”

Ya dora alhakin aukuwar kisan gillar da aka yi wa marigayi Ahmed Olalekan a kan hukumar gudanarwar makarantar wadda ya zarga da kin daukar matakin hana aukuwar lamarin.

Barazanar mayar da martani ya jefa mazauna kauyen Apete cikin firgici amma Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu da ke zaune a kauyen kuma yake rike da sarautar Otun Akogun Baale Morinbo ya yi wa Aminiya bayanin cewa, “A daidai lokacin aukuwar lamarin ne Baale na Apete ya sanar da ni, inda muka yi wani zama muka hanzarta sanar da jami’an tsaro suka zo suka kwantar da lamarin kafin ya kazance. An kashe dalibin ne a sashen Fanawole a kauyen na Apete, wanda yanzu haka muna zaune lafiya a cikin kauyen ba tare da wani firgici ba.”

Kakakin ’Yan sandan Jihar Oyo, ASP Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da aukuwar lamarin,  inda ya ce yanzu haka an kama wadansu dalibai da ake zargin ’ya’yan kungiyar asirin da ake zargi da haifar da rikicin.

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Abiodun Odude ya bayar da umarnin a girke jami’an tsaro da suke yin bincike a kan rikicin.