’Yan kungiyar asiri sun kone tsohuwa da gidanta a Legas

Wata tsohowa ta kone kurmus bayan da wasu kungiyoyin asiri biyu da ke gaba da juna suka yi karanbatta, inda suka sanya wuta a gidan da tsohuwar ’yar kimanin shekara 65 mai suna Adejoke Adefuye ke zaune a unguwar Bariga, Legas.A cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas, wasu ’yan kungiyar asiri ne […]

’Yan kungiyar asiri sun kone tsohuwa da gidanta a Legas
’Yan kungiyar asiri sun kone tsohuwa da gidanta a Legas

Wata tsohowa ta kone kurmus bayan da wasu kungiyoyin asiri biyu da ke gaba da juna suka yi karanbatta, inda suka sanya wuta a gidan da tsohuwar ’yar kimanin shekara 65 mai suna Adejoke Adefuye ke zaune a unguwar Bariga, Legas.
A cewar hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas, wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai wa abokan gabarsu farmakin ramuwar gayya, wanda hakan ya yi sanadiyyar kone tsohuwar. Tun da fari, rikincin ya barke ne a daren ranar Juma’ar da ta gabata, inda kashegari suka cinna wa gidan wuta.
Tuni dai aka mika gawarta zuwa gidan adana gawa, a yayin da wasu mutanen da ke zaune a gidan da suka samu raunuka kuwa, aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu.
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta yi nasarar kame ’yan kungiyar asirin su 8, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar tsohuwar, wadanda aka gurfanar da su a ranar Litinin da ta gabata, wadanda suka hada da madugun kungiyar, Tanimola Ogbere da Richard Abayomi sai Richard Ewa da kayode Dada da Afed Olajide; sai Nurudeen Latif da Mohammed Musa da Adamson Adelani. Harin ramuwar gayyar da ’yan kungiyar asirin suka kai wa abokan gabarsu ta yi sanadiyyar mutuwar Benmo da Abiye, wadanda abokan karawarsu ne, baya ga tsohuwar da ta kone kurmus.